Fitaccen Dan TikTok Ya Ga Ta Kansa a Kano bayan Ya Saki Bidiyo kan 'Kwanciya da Mata'
- Hukumar Hisbah ta Kano ta kama fitaccen 'dan TikTok, Namadina Tudunwada kan zargin yada sakonnin da ke karfafa zina
- Ana zargin ya kwatanta kudin aure da na zina a wani bidiyo da ya wallafa, wanda Hisbah ta ce kalamansa na iya jawo matasa su guji aure
- Hukumar ta gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta su guji wallafa abubuwan da ke saba wa tarbiyya da addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama fitaccen mai kirkirar bidiyoyin TikTok, Namadina Tudunwada, bisa zargin karfafa matasa su aikata zina ta hanyar sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Kano, Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
Abin da ya sa Hisbah ta kama Namadina
Leadership ta ra rahoto cewa sanarwar ta ce jami'an Hisbah da ke Tudunwada sun kama Namadina ne bayan wani bidiyo da ya wallafa ya yadu, inda ya kwatanta kudin aure da abin da ake kashewa wajen aikata zina.
A cikin bidiyon, an rawaito cewa Namadina ya ce zina na iya ci wa mutum kusan Naira 2,000, yayin da aure zai iya bukatar har Naira 200,000.
Hisbah ta ce irin wannan kwatanci na iya sa matasa su dauki zina a matsayin hanya mafi sauki da arha fiye da aure.
Hisbah ta ce kalaman sun saba wa tarbiyya
Hukumar ta zargi Namadina da wallafa sakonnin da za su iya karkatar da tunanin matasa tare da karfafa aikata abubuwan da suka saba wa tarbiyya da koyarwar addini.
Sanarwar ta ce:
"An kama wanda ake zargin ne bayan ya yi kalaman da za su iya yaudarar matasa tare da karfafa halayen da ba su dace ba."
Hisbah za ta fadada bincike
Mujahid Aminuddeen ya ce hukumar za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin kafin daukar matakin da ya dace bisa tanadin doka.
Ya ce:
"Za mu fadada bincikenmu tare da daukar matakin da ya dace bisa doka."

Source: Original
Hukumar Hisbah ta gargadi yan TikTok
Hisbah ta kuma gargadi sauran masu amfani da kafafen sada zumunta da masu kirkirar bidiyo da su guji wallafa abubuwan da za a iya fassara a matsayin karfafa rashin daa'a ko karya kyawawan dabi'un al'umma.
Hukumar ta jaddada cewa duk abin da ake wallafawa a kafafen sada zumunta na da tasiri, saboda haka ya kamata a tabbatar yana tafiya da tarbiyya da koyarwar addini.
Kotu ta daure dan TikTok Kano
A wani labarin, kun ji cewa wata kotun majistare da ke zaman ta a Kano ta daure dan TikTok, Abubakar Kilina a gidan kaso kan yaɗa badala.
An samu Kilina da laifin tallata dabi'u marasa kyau da kuma saka masu sanya kaya irin na mata watau yan daudu.
A daya daga cikin bidiyon TikTok dinsa an gano yadda yake amfani da kalmomin batsa wanda haka ya saba ka'ida da kuma al'adar Hausawa da jihar Kano.
Asali: Legit.ng

