'Saura Kiris': Gwamna Ya Tabbatar da Shirin Komawa APC bayan Jita Jitar Barin PDP

'Saura Kiris': Gwamna Ya Tabbatar da Shirin Komawa APC bayan Jita Jitar Barin PDP

  • Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya nuna maganar sauya shekarsa daga PDP zuwa APC na nan tafe kafin 2027
  • A wata ganawa da jama’a a Ukanafun, Fasto Eno ya kwatanta PDP da jirgin sama da ya lalace wanda ba zai iya tashi ba
  • Ya yi kira ga al'umma su ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa, ya raba tallafin motoci da kudi ga mutum sama da 400

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya fadi gaskiya kan jita-jitar ficewa daga PDP.

Gwamnan ya bayyana yiwuwar ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki nan ba da jimawa ba.

Gwamna ya yi magana kan shirin komawa APC daga PDP
Gwamna Umo Eno ya ce saura kiris ya bar PDP zuwa APC. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

Gwamna ya magantu kan shirin komawa APC

Gwamnan ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga taron jama’a a Ukanafun/Oruk Anam a makarantar QIC Central School, Ikot Akpankuk, cewar Leadership .

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta zama kamar jirgin da ya lalace kuma watakila bai da ikon kai shi inda ya nufa daga 2027.

Yayin da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborewori ya koma APC tare da magoya bayansa, Eno ya nuna cewa PDP ta rarrabu matuka kuma na iya durkushewa kwata-kwata.

Ya ce:

“Idan kana so ka yi tafiya da Ibom Airline, sai a ce kafin ta tashi ya samu matsala, ba za ka shiga wani jirgi ba?”
Gwamna ya magantu kan shirin barin PDP zuwa APC
Gwamna Umo Eno ya ce jirgin PDP ya gama lalacewa ba mai bari ta kife da shi. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

Gwamna ya ba al'ummarsa tallafin kasuwanci

Har ila yau, gwamnan ya bukaci jama’a su ci gaba da mara wa gwamnatinsa baya, ya ba da tallafi ga mutane fiye da 400, ciki har da kudaden kasuwanci, motoci da kyaututtuka.

Mutum 154 sun amfana da tallafin, sai na noma mutum 116, sannan mutum hudu duk sun karbi N5m.

Ya kuma bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace, yana gargadin su kada su lalata shi a damfara ko abinda bai dace ba.

Ya ce:

“Dole ne mu rika haduwa da mutane lokaci-lokaci mu saurare su, ba sai lokacin zabe kadai ba za mu rika zuwa wurinsu.
“Wannan ita c mazabar tarayya ta hudu da muka ziyarta, muna da guda shida kuma za mu kammala kafin sashen kasafi ya tsara bukatun kasafin 2026.
“Mu na duba bukatunku kuma za mu gaya muku wadanda za mu iya yi bisa ga abin da muke da shi. Wadanda ba mu iya yi yanzu ba, za mu saka su gaba.

Gwamna Eno ya ƙaryata shirin komawa APC

A baya, kun ji cewa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya musanta rade-radin cewa yana shirin barin PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kwamishinan yada labarai na jihar Akwa Ibom shi ya musanta cewa gwamna Eno zai bar PDP da ya lashe zabe a kai a farkon 2023.

Ya ce goyon bayan Eno ga Shugaba Bola Tinubu da Godswill Akpabio dabarar bunkasa hadin gwiwa ce domin amfanar da jama'ar jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.