Ganduje Ya Fadi yadda Guguwar Tinubu ke Shirin Gamawa da PDP a Najeriya

Ganduje Ya Fadi yadda Guguwar Tinubu ke Shirin Gamawa da PDP a Najeriya

  • An yi taron karbar gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa cikin jam'iyyar APC
  • Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa wasu gwamnonin PDP na dab da shiga APC a sakamakon nasarorin Bola Tinubu
  • Gwamna Otu na Cross River ya ce sauya shekar ya nuna yadda jama’a ke goyon bayan shugabancin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya karɓi Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, da wasu kusoshin jam’iyyar PDP zuwa APC.

Taron karɓar masu sauya shekar ya gudana ne a dandalin Cenotaph da ke Asaba, babban birnin jihar Delta, inda ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje
Ganduje ya ce gwamnonin PDP za su koma APC. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Abdullahi Ganduje ya ce wasu gwamnonin PDP za su shiga APC nan ba da daɗewa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauya shekar na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da fuskantar sauye-sauyen siyasa a Kudu maso Kudu, wadda PDP ta dade tana jan ragama a ciki.

Masu ruwa da tsaki sun shiga APC a Delta

Bayan wani taron sirri da aka yi a makon da ya gabata a Asaba, gwamnan Delta da mataimakinsa Monday Onyeme, da kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi sun koma APC.

Tuni ake kiran sauya shekar da “Guguwar Tinubu”, inda wasu ke ganin hakan wata alama ce ta neman kafa jam’iyya ɗaya a kasar nan.

Bayan shiga APC da Gwamna Oborevwori ya yi, yanzu jam’iyyar mai mulki na da gwamnoni uku a yankin Kudu maso Kudu — Edo, Cross River da Delta.

A yanzu haka Akwa Ibom da Bayelsa na hannun PDP yayin da makokamar Gwamnan Ribas da aka dakatar, Sim Fubara ke cikin ruɗani.

Ganduje: 'Wasu gwamnoni za su koma APC'

Yayin da yake mika tutar APC ga sabon gwamnan APC na Delta, Ganduje ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jagorancin da yake.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa hakan ne ya sa shugabanni da dama ke kaura zuwa APC a Najeriya.

Ganduje ya ce:

"Dole na yaba da gwamnoni 21 na jam’iyyar APC. Amma yanzu da wannan sauya shekar, mun samu na 22.
"Ku bude kunnuwa da kyau — domin wasu gwamnoni na dab da shigowa nan ba da jimawa ba.”

Ganduje ya ce karfin jam’iyyar APC yana karuwa a kowane yanki, musamman sakamakon manufofin Tinubu da ke janyo masa goyon bayan jama’a.

Otttu
Gwamna Ottu ya ce ayyukan Tinubu na saka mutane shiga APC. Hoto: Cross River State Government
Asali: Facebook

A nasa bangaren, Gwamna Bassey Otu na Cross River ya ce sauya shekar Oborevwori ba wai siyasa ba ce kawai, illa wani mataki na kishin kasa da neman ci gaban yankin Neja Delta.

Vanguard ta wallafa cewa gwamna Otu ya ce:

“Shigowarsa APC na nuna yadda jama’a ke kara amincewa da jagorancin Tinubu,"

Martanin El-Rufa'i kan sauya shekar gwamnoni

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce komawar gwamnoni APC bai dame su ba.

Nasir El-Rufa'i ya ce a zaben 2023 shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC suna da goyon bayan gwamnan Legas amma sun rasa jihar.

El-Rufa'i ya kara da cewa maganar hadaka na nan kuma da masu kada kuri'a kai tsaye suka dogara domin kifar da APC a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng