'Farko Kenan a Najeriya': Tinubu Ya Girgiza da Komawar Manyan Ƴan Siyasa APC daga PDP
- Shugaba Bola Tinubu ya ji dadin guguwar siyasa da ta kunno kai a Najeriya da jiga-jigan PDP suka dawo APC
- Tinubu ya bayyana sauyin jam’iyya daga PDP zuwa APC a Delta a matsayin “guguwar siyasa” mafi girma da aka taba gani
- Gwamna Sheriff Oborevwori da Ifeanyi Okowa sun ce sauyin ya yi daidai da bukatun Delta, inda suka yaba da kulawar Shugaba Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yaba da sauyin jam'iyya da ake samu daga PDP zuwa APC.
Tinubu ya bayyana cewa ba a taba samun irin haka ba a tarihin siyasar Najeriya bayan sauya shekar gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da mukarrabansa.

Asali: Twitter
Tinubu ya magantu da gwamna ya dawo APC
Jawabin Tinubu ya zo ne a wajen bikin sauyin jam’iyya na Gwamna Oborevwori da wasu PDP zuwa APC, a Cenotaph, Asaba da ke jihar Delta, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da sauyin jam’iyya daga PDP zuwa APC a Delta ke tayar da kura, Shugaba Tinubu ya ce hakan ba a taba ganin irinsa ba.
Sauyin jam’iyyar Sheriff Oborevwori da Ifeanyi Okowa da sauran manyan PDP ya kawo karshen mulkin PDP da ya dauki kusan shekara 26 a jihar.
Jiga-jigan da suka karɓi gwamna zuwa APC
Wadanda suka karbi sababbin 'yan APC sun hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu da Abdullahi Umar Ganduje da wasu gwamnoni.
Har ila yau, akwai Sanata Omo-Agege, Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, da Sanata Nwoko, Onowakpo-Thomas da sauransu.
Tinubu ya ce:
“Me ya fi wannan rana alfanu? Wannan guguwa ce ta siyasa da ba a taba gani ba a Kudu maso Kudu da kasar nan.
“Guguwa ce ta siyasa inda duk Sanatoci daga jihar suke APC, hakan ba a taba ganin irinsa ba a tarihin siyasar Najeriya.”
“’Yan Majalisar Wakilai da Gwamna da kwamitinsa da kansiloli kananan hukumomi 25 duk sun sauya sheka."

Asali: Facebook
Tinubu ya yaba da alaƙar Okowa, Oborevwori
Tinubu ya yaba wa tsohon gwamna Okowa bisa kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da magajinsa, yana mai kiransa babban shugaba, cewar Tribune.
A martaninsa, Gwamna Oborevwori ya ce:
“Sauyinmu zuwa APC ba na Delta kawai ba ne, na kasa baki daya ne, na yi imani da cewa wasu gwamnoni ma za su biyo baya. Idan kana da shiri, ba za ka kasa ba.
“Delta ba za ta tsaya a baya ba. Muna cikin adawa sama da shekaru 10. Shugaba ya nuna mana kauna, za mu rama.
Gwamna ya yi wa Tinubu alƙawarin miliyoyin kuri'u
Kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC tare da alkawarin kawowa Bola Tinubu kuri'u miliyan 1.4.
Oborevwori da mataimakinsa Monday Onyeme da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa da sauran jiga-jigan PDP sun koma APC a jihar Delta gaba ɗaya.
Rahotanni suka ce sauyin zai ƙarfafa APC a yankin Kudu maso Kudu, amma masana suna ganin samun kuri'un da gwamnan ke fata zai yi wahala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng