Guguwar APC: PDP Ta Tsorata da Sauya Sheka, Ta Sanya Ranar Taron Gaggawa
- PDP ta shirya taron gaggawa a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Abuja domin tattauna sauya sheƙa da sauran matsalolinta
- Jam’iyyar PDP ta rasa sama da 'ya'yanta 300 zuwa APC tsakanin Fabrairu 2024 da Fabrairu 2025 saboda rikice-rikicen cikin gida
- Majiyoyi sun ce jam’iyyar za ta tattauna batun sauya sheƙa, babban taron zaɓe, da shawarwarin da Gwamnonin PDP suka gabatar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – PDP ta fara ɗaukar mataki sakamakon guguwar sauya sheƙa da ta addabi manyan ‘yan jam’iyyar da kuma mabiyanta a 'yan kwanakin nan.
A tsakanin watan Fabrairu 2024 da Fabrairu 2025, fiye da yan PDP 300 sun sauya sheƙa zuwa APC, inda mafi yawan su suka yi hakan saboda rikice-rikicen cikin gida.

Asali: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NWC) na PDP ya shirya gudanar da wani taron gaggawa a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a zauna domin tattauna yadda ake fuskantar sauya sheƙa da sauran matsalolin cikin gida da suka addabi jam’iyyar a cikin ‘yan shekarun nan.
Yaushe PDP za ta yi taron gaggawa?
Setonji Koshoedo, sakataren riko da gwamnonin PDP suka naɗa, ya tabbatar da cewa za a gudanar da taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa a Abuja a ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa:
"Saboda bukatar da jama'a suka nuna da kuma bayan tattaunawa, an umarce ni da na kira taron NWC kamar haka: "Rana: Talata, 29 ga Afrilu, 2025. Wuri: Dakin taro na Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NWC), Wadata Plaza, Hedikwatar PDP ta Ƙasa, Abuja. Lokaci: Karfe 12 na rana."
Dalilin PDP na shirya taron gaggawa
Wata majiya a cikin kwamitin zartarwa na PDP ta bayyana cewa za a gudanar da taron ne domin neman mafita ga matsalolin da ke addabar jam’iyyar.

Asali: Facebook
Majiyar ta ce:
"Ba wani abu PDP za ta iya yi wajen hana masu niyyar barin jam’iyyar. Yawancin su suna sauya sheƙa saboda dalilai na kashin kansu, wasu kuma saboda suna da matsala da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa.
"Wane dalili gwamnan jihar Delta da sauran su suka bayar? Duk irin abin da PDP ta yi musu, sai da suka bar jam’iyyar."
"Lokacin taron, za a tattauna game da ci gaba da sauya sheƙa, shirye-shiryen manyan taruka da taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC), da kuma babban taron zaɓen shugabanni na ƙasa. Bugu da ƙari, za a duba shawarwarin da Gwamnonin PDP suka gabatar."
Majiyar ta tabbatar da cewa PDP za ta ɗauki matakan da za su fito da ita daga cikin matsalolin da ta ke ciki bayan taron.
An nemi PDP ta kori wasu 'ya'yanta
A wani labarin, kun ji cewa wani ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ideato, Ikenga Ugochinyere, ya ba da shawara ga jam’iyyar PDP don ta tsira da mutuncinsa.
Hon. Ugochinyere ya bayyana cewa gwamnoni biyu na PDP da kusan ‘yan majalisa 40 sun shirya ficewa daga cikin jam'iyyar zuwa APC mai mulki a kwanan nan.
Da yake jawabi ga manema labarai a Akokwa, Ideato ta Arewa a jihar Imo, Ugochinyere ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na cikin wani mawuyacin hali a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng