Abin da ya sa Kashim Shettima yake caccakar Atiku amma bai taba Kwankwaso da Obi
- Kashim Shettima ya ce yana da damar sukar Atiku Abubakar saboda wasan da yake tsakanin Bare-bari da Fulani
- Ya ce Peter Obi, Seyi Makinde, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi duk abokansa ne duk da bambancin siyasarsu
- Shettima ya bukaci ’yan Najeriya su sake zaɓen Bola Tinubu a 2027, yana mai kare manufofin tattalin arzikinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya ce zai ci gaba da sukar, Mai girma Atiku Abubakar.
Kashim Shettima ba zai raga wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba matuƙar yana sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
The Cable ta ce Kashim Shettima ya bayyana cewa yana da damar caccakar Atiku saboda asalinsa Fulani ne – abokin wasansu.
Mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan bayani aMaiduguri, babban birnin jihar Borno, yayin ƙaddamar da ayyukan NEDC.
A ranar Talata 24 ga watan Nuwamba 2026 aka kaddamar da wasu ayyuka da Hukumar Raya Arewa maso Gabas ta yi a jihar.
Dalilin da ya sa yake sukar Atiku
Shettima ya bayyana Atiku a matsayin dattijo a siyasa da yake girmamawa, amma ya ce kasancewarsa Bafullatani, abokan wasa ne.
Amma wasu sakarkaru da ba su da wani ilmin tarihi za su fitoo su ce, ‘Kai, ya taba zama Mataimakin shugaban kasa’, ka ajiye wasanku a gefe.
Ya ce:
“Atiku Abubakar dattijo ne da muke matuƙar girmamawa. Amma kasancewata Bafullatani, ina da damar tsokanarsu, kuma dole ne ya haƙura da duk tsokanar da zan yi masa.”
Ya kuma soki waɗanda suke ƙoƙarin nuna cewa bambancin ra'ayin siyasa yana nufin gaba da ƙiyayya tsakanin ’yan siyasa a Najeriya.
A cewarsa, muddin ’yan adawa ba su taba shugabansa, Bola Tinubu, zai ci gaba da mu'amala da su cikin mutunta juna in ji jaridar Punch.
Shettima ya ce Peter Obi, Seyi Makinde da Rabiu Kwankwaso da suke bangaren adawa abokansa ne.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba a taɓa jin yana zagin Peter Obi, Gwamna Seyi Makinde, ko tsohon gwamnan Kano ba don mutanensa ne.
Ya ce:
“Peter Obi abokina ne. Mun yi gwamna tare. Ban taɓa zagin gwamnan jihar Oyo ba. Abokina ne na ƙwarai. Haka ma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
“Kun taɓa jin na zagi Kwankwaso? Ba zan zage shi ba. Amma duk wanda ya kai wa shugabanmu hari, mu ma za mu mayar masa da martani.”
Shettima ya kuma bayyana cewa shi ma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, abokinsa ne.
Rikicinsa da Goodluck Jonathan kan Amaechi
Shettima ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawo rashin jituwarsa da Goodluck Jonathan shi ne goyon bayan da ya ba Amaechi a NGF.
An samu sabani da tsohon shugaban ƙasar lokacin takarar shugabancin ƙungiyar gwamnonin Najeriya.
Ya ce yana da kyakkyawar alaƙa da Amaechi duk da bambancin siyasa da yake tsakaninsu, ya kuma yi kira da a sake zaɓen Tinubu.
Shettima ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mara wa APC baya domin gwamnati mai-ci ta samu wa'adi na biyu kan karagar mulki.
Da yake bayani, Shettima ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa sun gaji tattalin arzikin da ke cikin mawuyacin hali.
https://punchng.com/why-i-criticise-atiku-but-dont-insult-obi-others-shettima/#google_vignette
Asali: Legit.ng


