Kawu Sumaila: Hadimin Buhari Ya Matsa Kwankwaso da Abba Su Koma APC

Kawu Sumaila: Hadimin Buhari Ya Matsa Kwankwaso da Abba Su Koma APC

  • Bayan sauya sheƙa da gwamnan Delta da wasu 'yan PDP suka yi, Bashir Ahmad ya bayyana cewa za su marabci Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf a APC
  • Hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed ya ce APC na shirin tarbar Kwankwaso, gwamna Abba da sauran mambobin NNPP na Kano
  • Hakan na zuwa ne bayan Sanata Kawu Sumaila da kusan dukkan jiga-jigan PDP a Delta sun koma APC bayan wani taro da aka yi a gidan gwamnati da ke Asaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - An fara samun sauyi a siyasar Najeriya bayan da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa suka fice daga PDP zuwa APC.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Kawu Sumaila daga Kano ya tabbatar da sauya shekar sa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Bashir
Bashir Ahmad ya ce za su karbi Kwankwaso zuwa APC. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso|Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana farin cikinsa da sauya shekar a wani sako da ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shi, jam’iyyar APC a Kano za ta tarbi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf idan suka yanke shawarar sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC

Batun sauya sheka zuwa APC a Delta

Sanata James Manager ya sanar da sauya sheƙar 'yan PDP na Delta a ranar Laraba bayan wani dogon taro da ya ɗauki sama da awa shida a gidan gwamnati da ke Asaba.

Ya bayyana cewa bayan gwamna Oborevwori, tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, kakakin majalisar jihar, shugaban PDP na jihar, da dukkan shugabannin kananan hukumomi sun koma APC.

Punch ta rahoto Sanata James Manager ya ce:

“Ina sanar da ku cewa ba za mu iya ci gaba da zama cikin jirgin da ke nitsewa ba,”

Bashir ya yi maraba da masu shiga APC

Bashir Ahmad ya bayyana cewa suna maraba da dawowar Oborevwori da sauran ‘yan siyasa zuwa APC.

Ya jaddada cewa hakan na nuni da yadda jam’iyyar ke karɓar mutane daga sassa daban-daban na ƙasa.

Hakazalika, Bashir ya nuna jin daɗinsa da dawowar Sanata Kawu Sumaila daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, yana mai cewa wannan na ƙarfafa jam’iyyar a yankin Kano ta Kudu.

Sumaila
Kawu Sumaila ya sauya sheka. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

APC za ta karɓi Kwankwaso da Abba Kabir

Bashir Ahmad ya ce APC a Kano na cigaba da shiri domin tarbar tsohon ministan tsaro, Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf idan suka sauya sheƙa daga NNPP.

Baya ga haka Bashir ya bayyana cewa a yanzu haka suna fatan jihohin Kano, Rivers da Bauchi su koma APC a gaba.

Yadda ake dandazon komawa APC

Tun bayan da jam’iyyar APC ta karɓi mulki a shekarar 2015, jam’iyyar ta kafa salon karɓar fitattun jiga-jigan siyasa daga manyan jam’iyyun adawa, musamman PDP da NNPP.

Wannan salon ya ƙara ƙarfafa APC a matakin jihohi da na ƙasa, tare da raunana ƙarfafa gwiwar ‘yan adawa.

A ‘yan shekarun nan, an sha ganin sauya sheƙa daga jiga-jigan PDP da NNPP zuwa APC, musamman a lokutan siyasar canjin gwamnati.

Gwamnonin jihohi, sanata, da shugabannin jam’iyyu na jihohi da ƙananan hukumomi sun koma APC domin sabbin dama ko rage matsin lamba daga hukumomi.

Yanzu haka, jam’iyyar APC na ci gaba da karɓar sabbin ‘yan siyasa, inda gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa suka koma APC tare da kusan dukan jiga-jigan PDP a jihar.

A Kano kuwa, Bashir Ahmad ya bayyana shirin tarbar Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC.

Wannan tsarin sauya sheƙa yana ƙara nuna ƙarfin APC a fagen siyasar Najeriya, sai dai yana kuma nuna raunin jam’iyyun adawa wajen tsare jiga-jigansu da samar da ingantaccen salo na fafutukar siyasa mai dorewa.

Legit ta tattauna da Musa Adamu

Wani dan Kwankwasiyya a jihar Kano, Musa Adamu ya zantawa Legit cewa zai cigaba da bin tafiyar Kwankwaso ko ya sauya sheka.

Musa Adamu ya ce:

"Dama mu Kwankwaso muke bi ba jam'iyya ba. Mun tabbatar duk matakin da zai dauka a siyasa ba zai hana shi kawo mana cigaba ba."

'Dan Hausa ya sauya sheka zuwa NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi mawakin Kwankwasiyya, Abubakar Sani 'Dan Hausa zuwa NNPP.

A watan Fabrairu ne 'Dan Hausa ya koma jam'iyyar APC bayan ya ziyarci Sanata Barau Jibrin a Abuja.

Bayan karbar Abubakar Sani, Sanata Kwankwaso ya kuma ziyarci ofishin jam'iyyar NNPP domin buda yadda ayyuka ke gudana a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng