APC Ta Shammaci Jama’a Inda Ta Lashe Dukkan Zaben Majalisa a Jihar PDP, An Sha Mamaki

APC Ta Shammaci Jama’a Inda Ta Lashe Dukkan Zaben Majalisa a Jihar PDP, An Sha Mamaki

  • Duk da rashin nasara a Kotun Koli, jam'iyyar APC ta bai wa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Delta mamaki a zabe
  • Jam'iyyar APC ta lashe dukkan zabukan cike gurbi na Majalisar jihar Delta inda ta yi wuji-wuji da PDP
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Delta ta lashe dukkan zabukan kujerun Majalisar jihar da aka gudanar.

Jam'iyyar ta shammaci PDP wacce ke mulkin jihar a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

INEC ta ayyana zaben Majalisar Tarayya a matsayin wanda bai kammala ba a jihar Arewa, akwai dalili

APC ta shammaci PDP inda ta lashe zabukan cike gurbi gaba daya
APC ta dawo da karfi bayan lashe zabukan cike gurbi a jihar Delta. Hoto: Ovie Omo-Agege, Sheriff Oborevwori.
Asali: Facebook

Wasu kujeru APC ta lashe a jihar Delta?

Jam'iyyar PDP mai mulkin ta gaza tunkarar APC wacce ta shirya tsaf kafin gudanar da zaben da dukkan karfinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da zabukan ne a kananan hukumomin Burutu da Ethiope ta Yamma a jihar, cewar Vanguard.

Jam'iyyar ta samu nasarar ce karkashin jagorancin tsohon mataimakin Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege.

Ovie ya tsaya takarar gwamnan jihar a zaben watan Maris na 2023 da aka gudanar inda ya yi rashin nasara.

Magoyan bayan PDP sun sha mamaki

Omo-Agege ya yi shiru a lamarin siyasar jihar tun bayan rashin nasara a Kotun Koli da ta bai wa Gwamna Sherrif Oborevwori na PDP nasara.

Tribune ta tattaro cewa Omo-Agege ya yi aiki tare da tsohon gwamnan jihar, James Ibori don kara wa jam'iyyar karfi gabannin zaben jihar.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da ɗan tsohon sifetan 'yan sanda wanda ya lashe zaben Majalisa, bayanai sun fito

Magoya bayan jam'iyyar PDP da dama ba su taba tsammanin haka ba inda suke tsammanin an kashe wa APC gwiwa a Kotun Koli.

APC ta lashe zaben ciyamomi a Borno

A wani labarin, jam'iyyar APC mai mulki a jihar Borno ta lashe zaben ciyamomin kananan hukumomi 27 da aka gudanar.

Har ila yau, jam'iyyar ta kuma lashe dukkan zabukan kansiloli 312 a jihar baki daya.

Bayan sanar da sakamakon zaben ne mace ta farko, Hajiya Inna Galadima ta zama shugabar karamar hukumar a jihar a tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel