Gwamna, Sanata da Mutanen da Suka Rabu da Adawa, Suka koma APC a Makon nan

Gwamna, Sanata da Mutanen da Suka Rabu da Adawa, Suka koma APC a Makon nan

A cikin shekarar 2025, jam'iyyar APC ta samu ƙaruwar yan siyasa da dama daga manyan jam'iyyun adawa, musamman PDP, NNPP da LP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Legit ta tattaro wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyun adawa da suka sauya sheƙa zuwa APC a makon da ake ciki.

Jam'iyya
Jiga jigan yan adawa sun koma APC Hoto: AbdulRahman Kawu Sumaila/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Ifeanyi Arthur Okowa
Asali: Facebook

Fitattun yan siyasar sun hada da:

1. Tsohon gwamna, Ifeanyi Okowa ya koma APC

The Cable ta ruwaito tsohon gwamnan Delta kuma mataimakin dan takarar shugaban kasa na PDP a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa ya sauya sheƙa zuwa APC a ranar 23 ga Afrilu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sanata mai wakiltar Delta South, James Manager, ya tabbatar da sauyin sheƙarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Amma da Legit ta tuntubi mashawarcin shugaban PDP na kasa, Yusuf Dingyadi, ya ce:

Har yanzu ba mu samu labarin ficewarsu daga PDP a hukumance ba. Mun dai ji an ce sun sauya sheka."

2. Gwamnan Delta ya sauya sheka zuwa APC

Punch ta wallafa cewa gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori tare da mataimakinsa Monday Onyeme da wasu kwamishinoni, sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Gwamnan Jihar Delta ya bayyana cewa:

“Za ku ji daga gare ni a ranar Litinin. Na riga na sanar da shugabannin kananan hukumomi na, kuma sun ce inda Mista Sheriff ya dosa, nan ma za su bi."
Delta
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya sauya sheka zuwa APC Hoton: Delta State Government
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda suka sauya sheka tare da gwamnan akwai tsohon Sanata mai wakiltar Delta ta Kudu, James Manager da wasu manyan PDP da ke jihar Delta.

3. Kananan hukumomin Delta sun koma APC

Gwamnatin Delta ta sanar da cewa shugabannin kananan hukumomin jihar 25 da kwamishinonin PDP a jihar sun sauya sheka tare da gwamnansu zuwa APC.

Kwamishinan yada labaran jihar,Aniagwu Charles ne ya tabbatar da haka ta cikin sanarwar da ya fitar.

Daya daga cikin shugabannin da suka bi gwamnan, ya ce:

“Inda Sheriff ya tafi, nan ma za mu tafi."

4. Kawu Sumaila ya kama hanyar shiga APC

Abdurrahman Kawu Sumaila, dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

Sanatan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar yammacin ranar Laraba, kwanaki bayan ya gana da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Ya ce matakin ya biyo bayan jajircewarsa na tabbatar da jin daɗin al’ummarsa da kuma cika alkawurran da ya ɗauka a matsayin wakilinsu a majalisar dattawa.

Ana sa ran zai sanar da cewa Sanata Kawu Sumaila zai bayyana cewa koma APC a hukumance, a cikin awanni ko kwanaki masu zuwa.

5.. 'Dan majalisar PDP ya koma APC

TVC News ta ruwaito cewa Shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar Wwakilai, Wole Oke, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP a jiar Osun. Wannan na kunshe a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 16 ga Afrilu, 2025, wacce ya aika wa shugaban PDP a mazabarsa da ke karamar hukumar Obokun, Oke.

Ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan tuntubar iyalansa da abokan hulɗarsa na siyasa, wadanda suka amince da hukuncin da ya yanke. Hon. Oke kuma aika da kwafen wasikar ga shugabannin jam’iyyar na matakin ƙasa, jiha da kuma ƙaramar hukuma.

Akwai alamun Fubara zai koma APC

A baya, mun wallafa cewa alamu na nuna cewa gwamnan Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, na shirin ɗaukar wasu matakai domin sassauta rikicin siyasar da ke addabar jihar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Landan yayin ziyararsa ta hutun kwanaki 18 zuwa ƙasashen Turai.

Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Fubara da kansa ne ya nemi ganawa da Tinubu domin tattaunawa kan rikicin siyasar Ribas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.