Siyasa Ta Yi Zafi: Takarar Obi da Kwankwaso Ta Ci Karo da Gagarumar Matsala

Siyasa Ta Yi Zafi: Takarar Obi da Kwankwaso Ta Ci Karo da Gagarumar Matsala

  • OK Movement ta fice daga haɗin gwiwarta da NDC, bayan rikicin siyasa da ya ɓarke tsakaninta da Peter Obi da jam’iyyar
  • Kungiyar ta sanar da dakatar da dukkan ayyukan kamfen da wayar da kan jama’a a matakin jihohi, ƙananan hukumomi da mazaɓu
  • OK Movement ta ce tana tattaunawa da wasu jam’iyyu da masu neman takarar shugaban ƙasa domin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Kungiyar siyasa ta OK Movement ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar siyasar da ta ƙulla da jam’iyyar NDC inda ta kawo ƙarshen dukkan ayyukan kamfen da tallata jam’iyyar nan take.

Kungiyar da ke goyon bayan tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a ƙarƙashin NDC, ta ce matakin ya biyo bayan lalacewar alaƙar siyasar da ke tsakaninta da Obi da jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun raɗawa Atiku sabon suna gabanin zaben shugaban ƙasa na 2027

Takarar Obi da Kwankwaso ta ci karo da matsala
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Dalilin OK na taba gari da Obi, Kwankwaso

A cikin wata sanarwa da ta fitar, darakta-janar na ƙungiyar na ƙasa, Hon. John Ozyl Ughulu, ya bayyana cewa shugabannin ƙungiyar sun samu sanarwar cewa Obi da NDC sun yanke shawarar kawo ƙarshen hulɗarsu da ita, cewar Vanguard.

Ughulu ya bayyana cewa abin takaici ne, amma ƙungiyar ta amince da matsayar tasu, inda ta yanke shawarar janye dukkan rassanta da goyon bayan ayyukanta daga jam’iyyar nan take.

Ya ce dukkan rassan ƙungiyar da ke matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi da jihohi ba za su ƙara shiga ayyukan kamfen da wayar da kan jama’a na NDC ba.

Babu mai juya kungiyar OK Movement

Darakta-janar ɗin ya jaddada cewa OK Movement ƙungiya ce mai zaman kanta, wadda babu wani mutum ko jam’iyyar siyasa da ke juya mata akalar harkokinta.

Ya ce:

“Bayananmu a bayyane suke. Tsarin rassanmu ne ke magana a madadinmu. Akidarmu ce ke bayyana ko mu wane ne.

Kara karanta wannan

Hare hare kan Obi, Kwankwaso ya fara tono boyayyun abubuwa, NDC ta yi gargadi

"OK Movement tana nan a matsayin ƙungiya mai cin gashin kanta, mai nata tsari da kuma yanke shawarar siyasa. Babu wani mutum, jam’iyyar siyasa ko masu wata muradin siyasa da suka mallaki wannan ƙungiya.”

Haka kuma, Ughulu ya nuna shakku kan yadda jam'iyyar NDC za ta iya mayar da farin jinin da take samu a kafafen sada zumunta zuwa ƙarfin da zai taimaka mata a zaɓe.

A kalamansa:

“Siyasa wasa ce ta lambobi, kuma lambobi suna taka muhimmiyar rawa wajen tantance ƙarfin jam’iyya, tasirinta a siyasa da kuma wanda zai yi nasara a zaɓe.”
Obi ya ci karo da matsala
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Ina makomar kungiyar OK Movement?

Duk da haka, kungiyar ba ta bayyana jam’iyyar da za ta koma ba, domin shugabanninta sun fara tattaunawa da wasu jam’iyyu da masu neman takarar shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.

Ughulu ya ce nan gaba ne za su sanar da jam’iyyar da ɗan takarar shugaban ƙasa da suka zaɓa domin mara wa baya.

Ya bayyana cewa ƙungiyar tana nazarin waɗanda za ta yi hulɗa da su ne bisa hangen nesansu, ƙwarewar shugabanci da kuma yadda manufofinsu suka dace da ƙa’idojin da take bi.

Kara karanta wannan

An ba Amurka da Turai goron gayyata su shigo harkokin siyasar 2027

Da yake bayyana irin shugabannin da ƙasar ke buƙata, Ughulu ya ce Najeriya tana buƙatar mutanen da za su iya warware saɓani, ƙarfafa haɗin kai da kuma fifita muradun al’umma a kan son zuciya.

Rikici ta barke a OK Movement

Kun ji cewa rikicin cikin gida ya ɓarke a ƙungiyar OK Movement mai goyon bayan takarar tsohon gwamna Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso a 2027.

Bangarori daban-daban da ke ikirarin shugabancin ƙungiyar sun fara musayar zarge-zarge a bainar jama'a duk da rokon da Peter Obi ya yi.

Masu ruwa da tsaki sun ce rikicin na cikin gida ne kuma ba zai hana shirye-shiryen zaɓen 2027 ba, kamar yadda Legit ta samu labari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.