Manyan Ƴan Siyasa, Jam'iyya da El Rufai Ya Ziyarta kafin Yanke Shawarar Barin APC
A ranar Litinin 10 ga watan Maris din shekarar 2025, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya koma jam'iyyar SDP.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nasir El-Rufai ya yi watsi da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya duba da matsalolin da ya ce su ke cikinta waɗanda ta gagara kawo karshensu.

Asali: Twitter
Hasashen abin da ya kori El-Rufai daga APC
Sai dai wasu na ganin tsohon gwamnan ya fice daga jam'iyyar ne saboda watsi da shi da aka yi a gwamnatin Bola Tinubu, cewar jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan alaka ta yi tsami tsakanin El-Rufai da APC da kuma gwamnatin Tinubu, tsohon gwamnan ke ziyarce-ziyarce na siyasa.
El-Rufai ya ziyarci manyan yan siyasa a Najeriya daga ɓangaren yan jam'iyyun adawa har da APC.
Tun farko an yi hasashen ziyarce-ziyarcen ka iya sanya El-Rufai neman mafaka a wata jam'iyyar adawa.
Legit Hausa ta duba muku manyan mutane da jam'iyyu da El-Rufai ya ziyarta kafin watsi da APC.
1. El-Rufai ya ziyarci ofishin jam'iyyar SDP
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ziyarci shugabannin jam'iyyar adawa ta SDP a Abuja.
Tsohon gwamnan ya kai wannan ziyarar a ranar Laraba, 20 ga watan Maris, 2024 yayin da aka yi ta raɗe-raɗin cewa yana shirin tattara ƴan komatsansa ya fice daga APC a wancan lokaci.
Wannan ziyara ta yi matukar daukar hankali a wancan lokaci saboda babu wanda ya yi tsammani El-Rufai zai ziyarci jam'iyya kamar SDP a daidai lokacin da yake APC.

Asali: Facebook
2. El-Rufai ya gana da Rabiu Kwankwaso
Jagoran jam'iyyar NNPP kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ban girma ga Nasir El-Rufai a ranar 28 ga watan Yunin 2024.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya kai ziyarar a gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna da ke garin Abuja domin su gaisa da juna.

Kara karanta wannan
El Rufai ya fara tone tone, ya fallasa makarkarshiyar da gwamnatin APC da ke kullawa
Kwankwaso ya wallafa hotunansu a shafin X, sai dai ziyarar ta jawo cece kuce a kafofin sada zumunta, har wasu ke alakanta hakan da shirin siyasa yayin da ake tunkarar 2027.
3. El-Rufai ya kai wa Buhari ziyara a Kaduna
Nasir El-Rufai ya yi tattaki har gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar 7 ga watan Maris, 2025 da muke ciki, cewar rahoton Punch.
Wannan ziyara na daga ziyarce-ziyarcen da El-Rufai ya yi yana daf da sanar da matakin ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan Buhari ya bar garin Daura a jihar Katsina domin komawa gidansa da ke Kaduna da zama.

Asali: Twitter
4. El-Rufai ya yi zama da Bakare da Aregbesola
Kwana ɗaya kafin barin APC, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai ziyara ga Rauf Aregbesola da Fasto Tunde Bakare a Lagos ranar Lahadi 9 ga watan Maris, 2025.
Mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana ziyarar a wani sakon X.
Ziyarar ta zo ne kwana kadan bayan El-Rufai ya gana da tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Kaduna.

Asali: Twitter
5. El-Rufai ya ziyarci Atiku Abubakar
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar domin buda baki a gidansa.
Ziyarar ta ja hankalin jama’a ganin cewa El-Rufa’i 'dan jam’iyyar APC ne, yayin da Atiku yake cikin masu shugabantar adawa a PDP.
Bayan ziyarar Atiku Abubakar ne tsohon gwamnan ya fitar da sanarwa a hukumance cewa ya fice daga jam'iyyar APC zuwa SDP mai adawa a Najeriya.

Asali: Facebook
An bukaci El-Rufai ya gurfana a kotun ICC
Mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya zargi Nasir El-Rufai da Muhammadu Buhari da kisan ƴan Shi'a a jihar Kaduna.
Sowore ya kuma zargi tsohon hafsan sojoji, Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya ce ya kamata su mika kansu ga kotun ICC domin fuskantar shari'a.
Wannan martani na Sowore na zuwa ne yayin da wasu ke ta murnar cewa El-Rufai ya koma SDP inda ya yi hasashen ana shirin hada shi da Yemi Osinbajo a zaben 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng