El Rufai Ya Fara Tone Tone, Ya Fallasa Makarkashiyar da Gwamnatin APC Ke Kullawa

El Rufai Ya Fara Tone Tone, Ya Fallasa Makarkashiyar da Gwamnatin APC Ke Kullawa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jefi jam'iyyar APC da zargin kawo ɓaraka a tsakanin ƴan adawa
  • Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa APC ce ke haddasa rikice-rikicen cikin gida da ke addaɓar jam'iyyun adawa a Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya nuna cewa jam'iyyar APC tana kitsa rikice-rikicen ne domin hana shugabannin jam'iyyun yin ayyukansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi sabon zargi kan jam'iyyar APC bayan ya fice daga cikinta.

Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki ce ke da hannu a rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa, ciki har da LP, PDP da NNPP.

El-Rufai ya zargi APC da kulla rikici a jam'iyyun adawa
El Rufai yace APC na da hannu a rikicin jam'iyyun adawa Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a sakatariyar jam'iyyar SDP a ranar Talata, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da barin APC, an bukaci El-Rufai, Buhari da Burutai su mika kansu ga ICC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin APC

El-Rufai ya yi iƙirarin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ce da gangan ke ɗaukar nauyin tayar da zaune tsaye a cikin waɗannan jam’iyyun domin raunana shugabancinsu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar LP an ƙirƙire shi ne kuma gwamnati ce ke ɗaukar nauyinsa, kowa ya sani."
“Yin yawo daga wannan kotu zuwa wannan na daga cikin dabarun da aka tsara domin shagaltar da shugabannin jam’iyyun daga yin aikinsu. Hakan ma na faruwa a PDP da ma a NNPP.”

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya taɓo batun rikicin NNPP

Nasir El-Rufai ya ci gaba da zargin cewa rikice-rikicen da ke faruwa a cikin NNPP, ciki har da batun korar babban jigon jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, an shirya su ne don haddasa ruɗani da raunata jam’iyyar.

“Abin ƙarshe da na karanta game da NNPP shi ne cewa wani ɓangaren jam’iyyar ya kori Kwankwaso da gwamnan da ke kan mulki."

Kara karanta wannan

Tsohon jigon APC ya fadi kuskuren El Rufai wajen komawa jam'iyyar SDP

"Idan ka ga irin waɗannan abubuwa, za ka san cewa rikicin ƙirƙiro shi aka yi. Wace jam’iyya ce ke korar gwamna mai ci, kuma shi kaɗai ne gwamnan da suke da shi?"
“Za ka san cewa an ƙirƙiro shi ne da gangan, ba ni da cikakken bayani, don haka ba zan iya ambatar sunaye ba.

- Nasir El-Rufai

Maganganun El-Rufai sun zo ne sa’o’i 24 bayan ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa APC ta kauce daga ainihin manufar da aka kafa ta a kai.

An buƙaci El-Rufai ya miƙa kansa ga ICC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya buƙaci Nasir El-Rufai ya miƙa kansa ga kotun hukunta masu aikata laifuffukan yaƙi ta duniya (ICC).

Omoyele Sowore ya buƙaci tsohon gwamnan ya miƙa kansa ga kotun ICC kan kisan da aka yi wa ƴan shi'a a shekarar 2015 a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng