'Wasu na Fama da Hawan Jini': Akpabio Ya Roki APC kan Wadanda Suka Rasa Tikiti
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya roƙi shugabannin APC su yi adalci wajen fitar da jerin 'yan takarar jam'iyya mai rinjaye
- Akpabio ya ce wasu daga cikin sanatoci da 'yan majalisar wakilai na fama da damuwa bayan sun rasa tikitin takara a zaɓen fitar da gwani
- Shugabannin APC sun nuna kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen Ekiti, tare da alƙawarin ƙara yawan ƙuri'un Gwamna Biodun Oyebanji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya roƙi Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam'iyyar APC kan zaben fitar da gwani.
Akpabio ya roki kwamitin da ya saurari korafe-korafen 'yan Majalisar Tarayya yayin fitar da jerin sunayen 'yan takarar ƙarshe bayan zaɓen fitar da gwani.

Source: Facebook
Akpabio ya yi wannan roƙo ne a wajen ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC domin tunkarar zaɓen gwamnan Ekiti mai zuwa, cewar Leadership.

Kara karanta wannan
Tsofaffin shugabannin majalisa da suka yi murabus daga APC kan zaben fitar da gwani
Godswill Akpabio ya roka wa wasu sanatoci alfarma
Ya ce wasu daga cikin abokan aikinsa suna fama da hawan jini saboda sakamakon zaɓen fitar da gwani.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mambobi 54 masu ci na Majalisar Tarayya sun rasa tikitin sake tsayawa takara bayan zaɓukan fidda gwani na APC da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasa.
Har ila yau, Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na APC bai amince da sakamakon mafi yawan zaɓukan fitar da gwani ba, baya ga na zaɓen shugaban ƙasa, inda ya musanta jerin sunayen 'yan takarar sanatoci da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Source: UGC
Rokon da Akpabio ya yi ga APC
Akpabio, wanda shi ne shugaban Majalisar Tarayya baki ɗaya, ya ce gwamnoni na da damar zaɓar 'yan majalisar jihohi da za su yi aiki tare da su, haka nan shugaban ƙasa ma yana da damar bayar da gudunmawa kan waɗanda za su yi aiki da shi.

Kara karanta wannan
Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe
Ya ce:
"Jam'iyya ita ce babba. Ina roƙon jam'iyya idan za ta fitar da jerin sunayen ƙarshe, ta tabbatar cewa kowa yana da wakilci. Wasu daga cikin mutanena suna fama da hawan jini saboda wannan lamari."
Ya ƙara da cewa bai kamata a matsa masa ya roƙi a saka sunan wanda ya sha kaye a fili ba, domin hakan yana nuna cewa mutumin ya yi rashin nasara a zaɓen fidda gwani.
Akpabio ya ce roƙon da yake yi ya ne bisa cancanta, ya kuma taya waɗanda suka yi nasara murna tare da jan kunnen abokan aikinsa su tabbatar sun shirya yadda ya kamata kafin shiga takara.
Ya ce idan jam'iyyar ta kammala zamanta, za su amince da sakamakon, tare da addu'ar Ubangiji Ya ba su nasara a babban zaɓe mai zuwa, cewar TheCable.
Akpabio ya ƙaryata batun taimakon sanatoci
Mun ba ku labarin cewa Majalisar dattawa ta yi magana game da alkwarin da aka ce shugabanta, Godswill Akpabio ya yi wasu sanatocin.
Rahotanni a baya sun bayyana cewa majalisa za ta duba wasu daga cikin sanatocin da suka fadi zaben fitar da gwani.
Akpabio ya ce ya nuna tausayi ne kawai ga wadanda suka sha kaye, ya ce APC na kokarin warware matsalolin da suka taso.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
