Kwankwaso: "Ficewar El Rufa'i daga APC Za Ta Saukaka wa Tinubu Tazarce"
- Kusa a APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ficewar Nasir El-Rufai daga jam'iyyar zai ba da damar sake tsari da kuma rage rikice-rikicen cikin gida
- Kwankwaso ya ce El-Rufai na iya jagorantar wasu tsofaffin gwamnoni da ministocin da suka yi aiki a zamanin Buhari domin ficewa daga APC
- Ya ba shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje shawarwari a kan hanyar da za a bi domin dakile tasirin ficewar tsohon gwamnan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Jihar Kano — Jigo a jam’iyyar APC reshen Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa ficewar Nasir El-Rufa'i daga jam’iyyar zai ba Bola Ahmed Tinubu damar yin tazarce cikin sauki a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne kwanaki kaɗan bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa APC, Nasir El-Rufa'i, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Kwankwaso ya ce ficewar El-Rufa'i tun da wuri zai bai wa APC damar sake tsara kanta da kuma tinkarar barazanar da za ta iya tasowa a nan gaba.

Kara karanta wannan
El Rufai ya fara tone tone, ya fallasa makarkarshiyar da gwamnatin APC da ke kullawa
Musa Kwankwaso ya yi wa El-Rufa'i uzuri
Kwankwaso ya nuna takaicinsa kan ficewar El-Rufa'i daga jam’iyyar, yana mai cewa dole ne a yi masa uzuri, ganin cewa bai samu mukami a gwamnatin Tinubu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Facebook
Ya ce irin wannan sauyi abu ne da ke faruwa a siyasa, kuma babu shakka jam’iyyar ba za ta ji daɗi ba idan ta rasa jiga-jiganta.
A cewarsa:
“A matsayinka na ɗan jam’iyya, idan ka rasa mutum ɗaya, tabbas za ka ji ba daɗi. Amma abin da nake cewa shi ne, wannan shi ne dai-dai gare mu.”
Kwankwaso: "Ficewar El-Rufa'i za ta ba Tinubu nasara"
Kwankwaso ya yi ikirarin cewa ficewar El-Rufa'i daga APC za ta bai wa jam’iyyar damar gano rauninta da kuma gyara matsalolinta kafin zaɓe mai zuwa.
Ya ce akwai rahotanni da ke nuna cewa tsohon gwamnan Kaduna zai jagoranci tawaga zuwa wajen tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin neman tubarraki.
Ya ƙara da cewa, baya ga El-Rufa'i, akwai tsofaffin gwamnoni da ministoci da suka yi aiki a zamanin Buhari da ake hasashen su ma za su iya ficewa daga jam’iyyar.
El Rufa'i: Musa Kwankwaso ya ba Ganduje shawara
Tsohon kwamishina a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukaci shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya kafa kwamiti na musamman don sasanta rikice-rikicen jam’iyyar a wasu jihohi.
Ya ce:
“Ya kamata a samar da kwamiti mai ƙarfi da zai daidaita rikice-rikicen jihohi, domin tabbatar da haɗin kai a jam’iyyar.”
Kwankwaso ya yi nuni da cewa a wasu jihohi kamar Binuwai, jam’iyyar APC na fuskantar matsaloli duk da cewa gwamnan jihar ɗan jam’iyyar ne.
Ya ce wajibi ne a rika yin tuntuba kan batun takara da sauran al’amuran siyasa domin daidaita jam’iyyar da kuma hana fitina.
Yadda El-Rufa'i ya bar APC zuwa SDP
A baya, kun samu labarin cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana Nasir El-Rufa’i a matsayin babban kadara ga jam’iyyar, ya jinjina masa.
Ya bayyana cewa amma akwai abubuwan da ya dace El-Rufa’i ya gyara domin inganta siyasarsa, yana mai cewa akwai yiwuwar su samu sabanin ra'ayi kan wasu batutuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng