Ana Hasashen Haɗaka a 2027, El Rufai Ya Ziyarci Tsohon Gwamna da Mutumin Buhari

Ana Hasashen Haɗaka a 2027, El Rufai Ya Ziyarci Tsohon Gwamna da Mutumin Buhari

  • Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai ziyara ga Rauf Aregbesola da Fasto Tunde Bakare a Lagos ranar Lahadi
  • Mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana ziyarar a wani sakon X
  • Ziyarar ta zo ne kwana kadan bayan El-Rufai ya gana da tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Kaduna
  • Wannan ziyara ta haifar da maganganu kan makomar siyasar El-Rufai da yiyuwar hadin gwiwa kafin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake tayar da kura bayan ya kai ziyara ga tsohon gwamna.

El-Rufai ya kai ziyara ga tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, da Fasto Tunde Bakare a Lagos a yau Lahadi.

El-Rufai ya gana da tsohon gwamnan Osun
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ziyarci Rauf Aregbesola a Lagos. Hoto: @MuyiwaAdekeye.
Asali: Twitter

El-Rufai ya ziyarci tsohon gwamna a Lagos

Kara karanta wannan

Barau ya karbi sakataren malaman Kwankwasiyya da 'yan uwan Abba a APC

Mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana hakan a wani sakon X a ranar Lahadi 9 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Adekeye ya ce El-Rufai ya zanta da tsohon gwamnan da kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Muhammadu Buhari a 2011.

Sanarwar ta ce:

“Malam Nasir El-Rufai ya kasance a jihar Lagos yau Lahadi don ziyartar Ogbeni Rauf Aregbesola da Fasto Tunde Bakare."
El-Rufai ya sake kai ziyara wurin tsohon gwamna a Najeriya
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ziyarci Rauf Aregbesola da wasu a Lagos. Hoto: Nasir El-Rufai.
Asali: Twitter

Ana ta hasashen dalilin ziyarce-ziyarcen El-Rufai

Wannan ziyarar El-Rufai ga wadannan mutane biyu ta biyo bayan wata ziyararsa ga tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna.

Ziyarar El-Rufai zuwa Lagos ta haifar da maganganu kan makomar siyasar sa da yiyuwar wasu dabarun siyasa kafin 2027.

Aregbesola, wanda tsohon gwamnan jihar Osun ne har na tsawon wa’adi biyu, ya bar jam’iyyar APC bayan rikici daya ki ci ya ki cinyewa a jihar.

Kara karanta wannan

'Na shiga motar Tinubu': Tsohon ɗan majalisa ya watsar da PDP, ya kama layin APC

Fasto Bakare kuwa, sananne ne wajen bayyana ra’ayoyin siyasa, kuma ya taba neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Legit Hausa ta yi magana da dan APC

Wani dan a mutum APC a Gombe, Ibrahim Mohammed Sila ya ce ai tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya dawo kamar Wike a PDP saboda matsalolin da yake haifarwa.

Ibrahim ya koka kan yadda El-Rufai ya ki barin APC kuma yana ta neman kawo mata cikas wurin ziyartar abokan gabanta.

Ibrahim ya ce:

"Shi kansa tsohon gwamna, Aregbesola ba dan APC ba ne bayan dakatar da shi da aka yi kuma hakan tarnaki yake kawo wa jam'iyyar."

Kwamishinonin El-Rufai sun magantu kan zargin badakala

Kun ji cewa tsofaffin kwamishinoni a mulkin Nasri El-Rufai a Kaduna sun musanta zargin da ake yi masu na karkatar da N1.37bn, tare da ikirarin ana kokarin bata masu suna.

Kwamishinonin sun soki umarnin kotu da ya amince a kwato adadin kudin daga wani asusu, kuma sun bayyana fargabar cewa ana kokarin zaluntar wasu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shigar da bukata a kotu don sahale mata ta kwato kudin da ta ce ta gano an karkatar da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng