"Muna da Mutane," APC Ta Hango Nasara a Jihar Ekiti da Zaben Shugaban Kasa a 2027
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam'iyyar na da karfin lashe zaben gwamnan Ekiti da na shugaban kasa a 2027
- Farfesa Yilwatda ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben APC na jihar Ekiti a Abuja
- Yilwatda ya mika tutar jam'iyya ga Gwamna Biodun Oyebanji domin neman wa'adi na biyu, inda ya ce APC na da mutane, kudi da karfin da za su ba ta nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar na da isasshen karfi da goyon baya da za su ba ta damar lashe zaben gwamnan Ekiti da kuma na shugaban kasa a 2027.
Yilwatda ya bayyana haka ne yayin kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben APC na jihar Ekiti a Abuja, gabanin zaben gwamna da za a gudanar ranar 20 ga watan Yuni, 2026.

Source: Twitter
Gwamna Oyebanji ya karbi tutar APC
Vanguard ta ruwaito cewa wajen taron, shugaban APC na kasa ya mika tutar jam'iyyar ga gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, wanda ke neman sake komawa mulki karo na biyu.
Ya ce gwamnan ya nuna kwarewa wajen aiwatar da ayyukan raya kasa, tallafin ilimi, inganta jin dadin jama'a da kuma inganta harkokin lafiya.
Farfesa Yilwatda ya ce:
"Kana zuba hanyoyin raya kasa kuma kana mamaye zukatan jama'ar jihar Ekiti. Muna alfahari da kai kuma muna godiya ga Allah da ya ba mutanen Ekiti da jam'iyyarmu shugaba irinka."
APC ta jaddada goyon bayan Oyebanji
Yilwatda ya bayyana Oyebanji a matsayin daya daga cikin mafi kyawun 'yan takarar da jam'iyyar APC ta tsayar.
Ya ce ayyukan da gwamnan ya yi sun sanya ya zama zabin da ya fi karbuwa a wajen al'ummar Ekiti, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
"Muna gabatar da kai ga mutanen Ekiti domin wa'adi na biyu. Jam'iyya tana alfahari da kai, kai ne daya daga cikin mafi kyawun 'yan takara a wannan zabe."

Kara karanta wannan
Wasu 'yan takarar gwamna na kashe Naira biliyan 20 zuwa 30 don su ci zabe a Najeriya
APC ta bayyana karfin da take da shi
Shugaban APC ya ce babu wata jam'iyya a Najeriya da za ta iya daidaita kanta da APC wajen yawan mutane, gogewa da karfin siyasa.
Ya kara da cewa jam'iyyar tana da cikakken shiri da kayan aiki domin samun nasara a zabukan da ke tafe.
"APC na da karfi kuma a shirye take ta lashe kowane irin zabe," in ji shi.

Source: Twitter
Yilwatda ya kuma bayyana cewa APC ba za ta fuskanci matsalar samun kudaden yakin neman zabe ba saboda tana da mutane masu karfi da za su iya samar da kudaden da ake bukata.
APC ta musanta sakin sunayen yan takara
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani kan rahoton da ke yawo cewa ta fitar da cikakken jerin sunayen 'yan takararta na majalisar dattawa a zaben 2027.
APC ta jaddada cewa jerin sunayen da ke yawo a dandalin sada zumunta da wasu kafafen intanet na ƙarya ne gaba ɗaya kuma ba su fito daga jam'iyyar ba.
Ta kuma yi kira ga mambobin jam'iyyar da masu ruwa da tsaki da su daina yada jerin sunayen domin suna haifar da ruɗani da yaudarar jama'a.
Asali: Legit.ng
