Kwana 1 da Barin APC, an Bukaci El Rufai, Buhari da Burutai Su Mika Kansu ga ICC

Kwana 1 da Barin APC, an Bukaci El Rufai, Buhari da Burutai Su Mika Kansu ga ICC

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya zargi Nasir El-Rufai da hannu a kisan fiye da 'yan Shi’a 300 a 2015
  • Omoyele Sowore ya bukaci a gurfanar da El-Rufai, Muhammadu Buhari da Tukur Buratai a gaban kotun ICC saboda laifuffukansu
  • 'Dan gwagwarmayar ya caccaki masu murna da sauya shekar da El-Rufai ya yi daga jam’iyyar APC zuwa SDP mai adawa
  • Sowore ya bayyana shirin El-Rufai da tsohon mataimakin shugaan kasa, Yemi Osinbajo na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mai rajin kare hakkin dan Adam, Omoyele Sowore, ya yi magana kan batun sauya shekar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Yele Sowore ya soki tsohon gwamnan kan kisan Shi’a fiye da 300 a shekarar 2015 lokacin mulkin Muhammdu Buhari.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa a SDP ya fadi yadda aka jawo El Rufai daga APC

Sowore ya bukaci Buhari da El-Rufai su mika kansu ga kotun ICC
Omoyele Sowore ya bukaci a hukunta Buhari da Nasir El-Rufai kan kisan kiyashi a Najeriya. Hoto: Nasir El-Rufai, Omoyele Sowore, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC zuwa SDP

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sowore ya ce Nasir El-Rufai ya cancanci gurfana a gaban kotun kasa da kasa ta ICC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa El-Rufai ya yi murabus tare da ficewa daga jam’iyyar APC a mazabarsa da ke garin Kaduna.

El-Rufai ya umarci magoya bayansa da su bi shi zuwa jam’iyyar SDP, yana mai sukar shugabancin APC.

A wata sanarwa da aka wallafa ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, El-Rufai ya zargi APC da barin manufofin cigaban da aka gindaya tun farko.

Sowore ya zargi El-Rufai, Buhari da kisan kai

Ya ce El-Rufai tare da tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon hafsan sojoji, Tukur Buratai, sun aikata kisan gilla ga ‘yan Shi’a.

Sowore ya bayyana cewa an birne waɗanda aka kashe a kaburburan da ba su da zurfi bayan rundunar soji ta yi musu kisan gilla.

Kara karanta wannan

El Rufai ya girgiza siyasar Najeriya, manyan jiga jigan APC na shirin komawa SDP

A cikin rubutun ya yi zargin cewa:

"An kama tsohon shugaban kasar Philippines, Duterte bayan umarnin kotun ICC saboda kisan gilla kan yan Adam, amma a nan Najeriya ana ta murna game da Nasir El-Rufai.
"A daidai lokacin da ya kamata da shi da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon hafsan sojoji, Buratai su mika kansu ga kotun ICC saboda kisan gilla da suka yi wa 'yan Shi'a."
Sowore ya zargi ana neman kakaba Osinbajo a mulkin Najeriya
Omoyele Sowore ya ce akwai shirin da ake yi na hada Osinbajo da El-Rufai a shugabancin Najeriya. Hoto: Prof. Yemi Osinbajo.
Asali: Twitter

2027: Sowore ya yi hasashen takarar Osinbajo

Sowore ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ke murna da sauyin jam’iyyar El-Rufai zuwa SDP maimakon a bukaci ya fuskanci hukunci.

Ya bayyana cewa akwai yunkurin da ake yi na tsayar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar shugaban kasa.

A cewarsa:

"Kwanan nan za su fara yaba wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bai tabuka komai ba a siyasa domin shirin komawa SDP."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan sauya sheƙar El Rufai daga APC zuwa SDP

Ya ce ana shirin hada El-Rufai da Osinbajo a matsayin Shugaba da Mataimaki a zaben 2027 don saukaka wa Tinubu hanya.

Ramadan: Sowore ya soki wasu gwamnonin Arewa

Kun ji cewa dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya soki gwamnonin Arewa kan rufe makarantu yayin azumin Ramadan, yana mai cewa hakan jahilci ne.

Sowore ya ce ko Saudiyya ba su rufe makarantu saboda azumi, yana cewa shugabannin Najeriya sun jahilci addini kuma ba su fahimci ilimi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng