Trump Ya Dakatar da Sojojin Amurka Kai Hari a Iran bayan Samun Gargadi
- An yi musayar hare-hare tsakanin Amurka da Jamhuriyar musulunci ta Iran duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da ake da ita
- A ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026, Shugaba Trump ya bayyana cewa ya soke hare-haren da Amurka ta shirya kaiwa a Iran
- Shugaban kasar na Amurka ya nua cewa za a sanya hannu tsakanin kasashen biyu don kawo karshen yakin da aka fara a watan Fabrairun 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump a ranar Alhamis ya bayyana cewa ya soke shirin kai hare-hare kan ƙasar Iran.
Shugaba Trump ya nuna lamun yiwuwar sanyawa wata yarjejeniya hannu da mahukunta a Tehran bayan tattaunawa ta kai matakin ƙoli.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026.
Meyasa Trump ya soke kai hari a Iran?
Trump ya bayyana cewa ya soke kai hare-haren ne bayan ci gaban da aka samu a tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu.
“Bisa ga gaskiyar cewa tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai ga mataki mafi girma na shugabancin Iran kuma an amince da ita, na… soke hare-hare da bama-baman da aka tsara kai wa Iran a wannan maraice."
“Za a sanar da lokaci da kuma wurin da za a sanya hannu nan ba da jimawa ba."
- Shugaba Donald Trump
Sai dai, Trump ya ce za a ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwan Iran har sai an kammala cimma yarjejeniya.
Iran ta yi gargadi kan Amurka
Tun da fakro Iran ta gargaɗi Washington a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026 cewa tana fuskantar haɗarin shiga cikin “gagarumin ruɗani marar ƙarshe” na yaƙi da kuma tashin gwauron zabi na farashin makamashi.
Gargadin na zuwa ne bayan da Trump ya sha alwashin ƙaddamar da sabon zagaye na hare-haren sama a da kuma ƙwace wani rumbun mai da ke kan tsibiri a Iran, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan
Mele Kyari: Kwamitin majalisa ya umarci cafke tsohon shugaban NNPCL kan badakalar N210trn

Source: Facebook
Babban mai jagorantar tattaunawa a Iran a tattaunawar da ake yi da Amurka, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya fitar da gargaɗin bayan da ɓangarorin biyu suka yi musayar wuta a cikin dare kuma Trump ya yi barazanar cewa dakarun Amurka za su yi barna “mai tsanani a daren nan".
Yaƙin, wanda ya fara a ranar 28 ga watan Fabrairu tare da jerin hare-haren Amurka da Isra'ila a kan Iran, an dakatar da shi ne a ƙarkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Afrilu, amma ƙoƙarin cimma tabbataccen ƙarshen faɗan ya tsaya cak tun daga lokacin.
Trump ya yi barazana ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaba Trump ya ce kasar Iran ‘ta ɗauki lokaci mai tsawo’ kafin ta cimma yarjejeniya saboda haka za ta dandana kudarta.
Hakazalika, Trump ya sake jaddada iƙirarin cewa an wargaza dakarun sojojin Iran, kuma rundunoninsu na ruwa da na sama ba su aiki.
Asali: Legit.ng
