Za a Gudanar da Zaben Cike Gurbi a Kebbi, INEC Ta Tantance Jam’iyyu 2 kacal
- Hukumar INEC ta bayyana cewa APC da LP ne kadai jam'iyyun da za su shiga zaben cike gurbi na majalisar jihar Kebbi a Zuru
- INEC ta ce jam’iyyun biyu ne kacal suka cika sharuddan mika sunayen ‘yan takara kafin wa’adin da hukumar ta kayyade
- Akalla masu kada kuri’a 109,292 ne za su shiga zaben yayin da INEC ta horar da ma’aikata 822 domin gudanar da zaben lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kebbi - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa jam’iyyun APC da LP ne kadai suka cancanci shiga zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar da za a gudanar a karamar hukumar Zuru.
Kwamishinan zabe na jihar Kebbi, Abubakar Sarkin Pawa Dambo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen zaben.

Source: Twitter
INEC: Jam’iyyun da suka shiga zaben Kebbi
Dambo ya ce hukumar ta ware tsakanin ranar 22 zuwa 26 ga watan Mayu 2026 domin jam’iyyun siyasa su gabatar da ‘yan takararsu kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanada, in ji rahoton Daily Trust.
Sai dai ya ce bayan karewar wa’adin, APC da LP ne kadai jam'iyyun da suka cika dukkan sharuddan da INEC ta gindaya domin amincewa da ‘yan takararsu.
“Saboda haka jam’iyyun biyu ne kawai za su shiga zaben cike gurbin, sannan ana bukatar su mika sunayen jami’an kula da rumfunan zabe kafin ranar 10 ga watan Yuni.”
- Abubakar Sarkin Pawa Dambo.
Ranar fara kamfen da zabe
Kwamishinan zaben ya bayyana cewa yakin neman zabe zai fara nan take kuma zai kare a ranar 18 ga watan Yunin 2026.
Ya kara da cewa za a gudanar da zaben cike gurbin ne a ranar 20 ga watan Yuni. A cewarsa, za a yi amfani da tsohon kundin masu kada kuri’a yayin gudanar da zaben.
Mutanen da za su kada kuri’a
Abubakar Dambo ya ce za a gudanar da zaben a mazabu 10 da rumfunan zabe 200, inda shida daga cikin mazabun suke a cikin garin Zuru.
Ya bayyana cewa mutum 109,292 masu rijistar zabe ne ake sa ran za su kada kuri’a, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Source: Original
Kwamishinan zaben ya ce:
“Mun horar da ma’aikatan wucin gadi 822 domin tabbatar da gudanar da zabe cikin nasara a ranar 20 ga watan Yuni, 2026."
Dambo ya kuma yi kira ga wadanda suka cancanci yin rajistar zabe ko canja wurin katinsu su ci gaba da zuwa cibiyoyin rajista domin yin hakan.
Taron masu ruwa da tsakin ya samu halartar jami’an tsaro, jam’iyyun siyasa, kungiyar mata ta NCWS da sauran mahalarta.
Kakakin Majalisar jihar Kebbi ya rasu
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, Shugaban majalisar dokokin jihar, Muhammad Usman Zuru, ya rasu a daren Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan
Wasu ƴan siyasa na daf da rasa tikitinsu, INEC ta yi watsi da wasu zaben fitar da gwani
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Masar inda yake karbar magani kan wata cuta da ba a bayyana ba.
Marigayin ya kasance wakilin mazabar Zuru a majalisar dokokin Jihar Kebbi, kuma ana kallonsa a matsayin daya daga cikin jiga-jigan majalisar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

