Hotuna: Ruwan Sama Kamar da Bakin Kwarya Ya Yi Gyara a Bauchi, An Rasa Rayuka
- Ruwan sama mai karfi da ya haddasa ambaliya ya yi sanadin muduwar wata mata mai shekaru 50 da jikarta a jihar Bauchi
- Mazauna yankin sun ce ruwan ya gangaro ne daga wani gari da ke makwabtaka da su inda ya lalata gidaje da dukiya mai yawa
- Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa jami’anta sun kai ziyara wurin domin tantance barnar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bauchi - Wata mummunar ambaliya da ta biyo bayan ruwan sama da iska mai karfi ta kashe wata mata da jikarta a kauyen Bara da ke karamar hukumar Kirfi a jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa mamatan sun hada da Aisha Sagir mai shekaru 50 da jikarta Aisha Shuaibu mai shekaru hudu, dukkaninsu mazauna Unguwar Katsinawa ne a kauyen Bara.

Source: Getty Images
Yadda ambaliya ta yi barna a Bauchi
Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Nasiru ya shaidawa Daily Trust cewa mamakon ruwan sama da aka yi ya jawo ruwa ya balle daga wani bangare na kauyen Jambba.
A cewarsa, ruwan ya kwararo da 'karfin tsiya', lamarin da ya haddasa lalacewar gidaje, mutuwar dabbobi da asarar dukiyoyi masu yawa.
Nasiru ya ce:
“Ruwan ya shigo da karfi daga wani wuri da ba a sani ba, ya lalata gidaje da hallaka dabbobi, babu wanda ya yi tunanin ruwa zai shigo daga wannan bangaren na Bara.
“Ruwan ya mamaye gidaje tare da kashe mutum biyu ciki har da wata matar aure mai shekaru 50 da jikarta a Unguwar Katsinawa.”
Martanin 'yan sandan Bauchi
Muhammad Nasiru ya kara da cewa baya ga asarar rayuka da dukiyoyi, mutane da dama sun rasa matsugunansu sakamakon barnar da ambaliyar ta yi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Nafiu Habib, ya fitar.
A cikin sanarwar, Habib ya ce:
“Da misalin karfe 10:00 na safiyar yau, 10 ga watan Yunin 2026, karamar hukumar Kirfi ta fuskanci ruwan sama mai karfi tare da iska.
“Lamarin ya yi sanadin mutuwar Aisha Sagir mai shekaru 50 da jikarta Aisha Shuaibu mai shekaru hudu, dukkaninsu mazauna Unguwar Katsinawa a kauyen Bara.”
Ya kara da cewa ruwan ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin naira yayin da ya ce ‘yan sanda daga ofishin Kirfi sun kai ziyara yankin domin tantance barnar da tabbatar da zaman lafiya.

Source: Facebook
Hotunan barnar da ambaliyar ta yi
Gidan rediyon Albarka FM da ke Bauchi, ya wallafa hotunan yadda wannan ambaliya ta yi barna da kuma daukin da mutane suka kai a yankunan da abin ya shafa.
Kalli hotunan a nan kasa:
Jihohi 33 za su fuskanci ambaliya
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya a Najeriya.
Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026.
Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu.
Asali: Legit.ng


