Kwankwaso Ya Magantu kan Rikicin 'Yan Kwankwasiyya da Mutanen Atiku
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan yadda 'yan Kwankwasiyya ke takun saka da magoya bayan Atiku Abubakar
- Tun bayan ficewar Rabiu Kwankwaso daga ADC zuwa NDC aka fara musayar yawu tsakanin 'yan Kwankwasiyya da mutanen Atiku
- A bayanin da ya yi, Kwankwaso ya bayyana cewa ba shi da wata mummunar alaka da Atiku, kuma bai horar da mutane kan zaginsa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan rashin jituwar 'yan Kwankwasiyya da mutanen Atiku Abubakar.
Kwankwaso ya ce bai horar da 'yan Kwankwasiyya su yi zagi ko cin mutuncin wani dan siyasa ba ko da tafiyar su ba daya ba ce.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Kanon ya yi bayani ne a wata hira da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na X game da lamuran siyasar Najeriya a yau.
Alakar Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso
A kan alakar da mutanen Atiku da 'yan Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya ce dama ba a raba siyasa da ce-ce-ku-ce ba da kananan maganganu.
Duk da haka, Kwankwaso ya ce kowa ya san ba zai tara 'yan Kwankwasiyya ya ce su je su soki Atiku Abubakar ba saboda wata manufa ta siyasa.
Ya kuma bayyana cewa ba tarbiyar Kwankwasiyya ba ne sukar mutane kuma shi ma bai sukar Atiku Abubakar a harkokin siyasa.
Ya ce:
"Na san kowa ya san ba zan je in ce da magoya baya na ku je ku soki Atiku ba, kuma ni ba na sukar sa, ba na zaton shi kan sa mai girma Wazirin Adamawa zai tara mutanensa ya ce su je su tsokani yara na da sauransu."

Kara karanta wannan
"Me kuma suke so"; Ana neman tunzura jagoran NDC kan tikitin Obi da Kwankwaso a 2027
Tarbiyyyar 'yan Kwankwasiyya
Da ya ke karin bayani kan 'yan Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya ce duk tafiya ba a rasa fitinannu masu ganin ya kamata a rika tayar da fitina a harkokin siyasa.
Ya ce:
"Abin da na sani, musamman tarbiyyar da muka yi wa magoya bayan mu, in dai dan Kwankwasiyya ne, shi ne kar ka je ka tsonaki kowa."

Source: Facebook
Legit ta tattauna da Musa Hassan
Wani mai goyon bayan Atiku Abubakar, Musa Hassan ya bayyanawa Legit Hausa cewa abubuwan da suke faruwa galibi saboda siyasa ake yin su ba saboda gaba ba.
Ya ce:
"Siyasa dama ta gaji haka, wani lokaci a kan samu sabani da rashin jituwa. Amma dai duk da haka wasu daga cikin dukkan bangarorin suna zafafawa."
"Kwankwaso ya yi magana mai kyau. Na yaba masa matuka."
Magana kan manoman Najeriya
Wani abu da Rabiu Kwankwaso ya yi tsokaci a kai shi ne batun manoman Najeriya, inda ya ce gwamnatin tarayya ta kashe harkokin noma a kasar nan.
Ya koka da cewa yanzu haka kudin buhun taki daya ya kai darajar buhun masara uku, wanda ya ce a gwamnatin baya akasin haka ne.
Ga bidiyon hirar da aka yi da Kwankwaso:
Maganar Kwankwaso kan tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan yadda 'yan ta'adda ke cigaba da cin karensu babu babbaka a fadin Najeriya.
Kwankwaso ya ce a yanzu haka masu garkuwa da mutane, barayi, 'yan fashi da makami da sauran 'ya ta'adda na cigaba da kai hare-hare a jihohi da dama a kasar nan.
Ya bukaci Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta tashi tsaye wajen magance matsalolin tsaro, yana cewa abu ne da za a iya kawo karshen sa.
Asali: Legit.ng

