'PDP za Ta Dawo Mulki a 2027,' Martanin Jama'a kan Ziyarar El Rufa'i ga Atiku

'PDP za Ta Dawo Mulki a 2027,' Martanin Jama'a kan Ziyarar El Rufa'i ga Atiku

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar domin buda baki
  • Ziyarar ta ja hankalin jama’a ganin cewa El-Rufa’i 'dan jam’iyyar APC ne, yayin da Atiku yake cikin masu shugabantar adawa a PDP
  • Wasu daga cikin masu amfani kafafen sada zumunta sun bayyana ra’ayinsu kan ziyarar, suka tofa albarkacin bakinsu game da lamatin
  • Legit ta tattauna da wani matashi dan jam'iyyar PDP domin jin ra'ayinsa kan yadda Atiku ke kokarin kulla alaka da 'yan adawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, lokacin cin abincin buda-baki.

A cikin tawagar El-Rufa’i har da tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, da kuma Musa Halilu, Dujima Adamawa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Sokoto ya koma jam'iyyar SDP don ƙulla sabon ƙawance da El Rufai?

Atiku
El Rufa'i ya yi buda baki a gidan Atiku. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Legit ta gano yadda ziyarar ta gudana ne a cikin wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufa'i ya ziyarci Atiku Abubakar

Hirar siyasa ta kara dawowa sabuwa kan Nasir El-Rufa'i bayan ya kai wa wasu 'yan hamayyar Tinubu ziyara, ciki har da Atiku Abubakar.

Ziyarar ta jawo ce-ce-ku-ce, kasancewar El-Rufa’i jigo ne a jam’iyyar APC, yayin da Atiku Abubakar yake tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023.

Abin da mutane suka fada kan ziyarar

Ziyarar El-Rufa’i ga Atiku Abubakar ta haddasa martani iri-iri daga jama’a a shafukan sada zumunta.

Wasu na ganin hakan alama ce ta sabuwar hadaka a siyasa, yayin da wasu ke bayyana shakku game da dalilin ziyarar.

Wani mai amfani da Facebook, Abdullahi Iliya Maigado, ya yi gargadi ga Atiku, yana mai cewa:

"Ya mai girma, ka bude ido, saboda wadannan da suka ziyarce ka ba su taimaka maka lokacin da ka ke bukata ba. Amma yanzu da suka rasa yadda za su yi, sai suka zo gare ka."

Kara karanta wannan

Kwana 1 da barin APC, an bukaci El-Rufai, Buhari da Burutai su mika kansu ga ICC

Alakar ziyarar da siyasar 2027

A yayin da wasu ke nuna shakku, wasu kuwa sun yi fatan samun sakamako mai kyau kan ziyarar.

Shitu Garba Bara ya ce:

"Wannan mataki zai kawo alkhairi ga ‘yan Najeriya, In sha Allah."

Hakazalika, Sa’ad Isma’il Bala Kaura da Abdurrashid Namalam Dankanjiba sun bayyana cewa hadin kan da ake samu na iya dawo da jam’iyyar PDP a mulki a shekarar 2027.

"Muna da yakinin PDP za ta sake dawowa kan mulki, Insha Allah, a 2027,"

- Sa’ad Isma’il Bala Kaura

ElRufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Kaduna State Government
Asali: Twitter

Wasu sun yi addu’a da fatan alheri

Yusuf Kaoje ya nuna godiya kan wannan haduwa, yana mai cewa:

"Masha Allah! Ci gaba da aiki. Da ikon Allah sakamakon zai zama abin alfahari. Mu hada kai domin dawo da martabar Najeriya."

Shi ma Okafor Anthony ya yi addu’a tare da fatan alheri ga dukkan mahalarta ziyarar, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa a SDP ya fadi yadda aka jawo El Rufai daga APC

"Ina yi muku fatan alheri a cikin azumin Ramadan. Matsayinku a siyasa da kuma yadda kuke dagewa kan ibada na nuna nagartarku."

Ziyarar dai ta bar mutane cikin mamaki da tunani kan abin da ke tafe a siyasar Najeriya, musamman a tsakanin manyan ‘yan siyasa da jam’iyyun adawa.

Legit ta tattauna da dan PDP

Wani matashi dan jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Bilyaminu Yahaya ya ce alakar Atiku da 'yan adawa abu ne mai kyau.

Matashin ya ce:

"Muna farin ciki da yadda lamura suka fara canjawa a siyasance. Hadakar 'yan adawa abu ne da za mu yi farin ciki da shi. Muna fatan za a samu hadin kai a gaba."

Atiku ya ce bai sauya sheka ba

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce har yanzu yana cikin PDP, akasin jita-jitar da ak ji.

Alhji Atiku Abubakar ya yi bayanin ne yayin da aka fara yada jita jitar cewa ya sauya sheka, ya fita daga jam'iyyar PDP zuwa SDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng