Cikakken Bayani: Nasir El Rufai Ya Fitar da Sanarwar Ficewa daga APC zuwa SDP

Cikakken Bayani: Nasir El Rufai Ya Fitar da Sanarwar Ficewa daga APC zuwa SDP

  • Bayan shekaru 12 a APC, tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP da ya dade yana raba a Najeriya
  • El-Rufai ya bayyana cewa da shi aka kafa APC amma jam'iyyar ta sauka daga manufofinta na usuli shiyasa ya ga lokaci ya yi da za su raba gari
  • Tsohon gwamnan ya ce zai ci gaba da ƙoƙarin jawo manyan ƴan adawa domin su kawo ƙarshen APC a dukkan zaɓukan da za a yi daga nan zuwa 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya tabbatar da batun ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Malam Nasir El-Rufai ya kuma bayyana komawa jam'iyyar SDP, wanda ya ce za su haɗa ƙarfi da karfe wajen ƙalubalantar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

'Mutuwa ce kawai za ta raba ni da APC,' Tarihi ya tuna maganganun El Rufa'i

Malam Nasir El-Rufai.
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai ya fitar da sanarwa da kan batun ficewa daga APC Hoto: @Elrufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya ce ya miƙa wasiƙar murabus dinsa daga APC a mazabarsa da ke Kaduna, kuma sai da ya yi shawara abokansa, da magoya baya kafin yanke wannan mataki.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, El-Rufai ya bayyana cewa ya yi imanin cewa jam'iyyar APC ta kauce wa manufofin ci gaba da aka kafa ta a kai.

Sanarwar da El-Rufai ya fitar a shafinsa

Tsohon gwamnan ya ce:

"A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC, da ni da wasu masu kishi muka zauna har aka cimma haɗewar jam’iyyun siyasa da suka haifar da APC."
"Tun daga shekarar 2013, ba ni da fatan da ya wuce ganin ɗabi'ata ta daidaita da manufofin APC har zuwa lokacin da zan yanke shawarar yin ritaya daga siyasa.

Kara karanta wannan

Daga sauya sheka, El Rufa'i ya fadi yadda zai jawo rugujewar APC a Najeriya

"Sai dai abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu da suka gabata sun tabbatar da cewa waɗanda ke da iko a jam’iyyar a halin yanzu ba su da sha’awar gane, balle magance matsalolin da APC ke fuskanta."

Gudummuwar da El-Rufai ya ba jam'iyyar APC

"A matsayina na ɗan jam’iyya mai biyayya, na taka muhimmiyar rawa wajen ganin APC ta samu nasara a zaɓukan 2015, 2019 da 2023.
A matsayin gwamna a ƙarƙashin APC daga 2015 zuwa 2023, na yi bakin ƙoƙari wajen aiwatar da manufofin ci gaba, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, inganta daidaito a damammaki, samar da ayyukan yi da jawo jarin kasuwanci.
"Amma irin waɗannan manufofin da nake tinkaho da su sun rasa daraja a APC ta yanzu, wacce a cikin shekaru biyu da suka gabata ta hana mambobinta motsi kuma ta raina su. Wannan abu ne da ba zan iya amincewa da shi ba.

Kara karanta wannan

"Mai jiran gado": Martanin 'yan Najeriya bayan El Rufai ya fice daga APC zuwa SDP

- Nasir El-Rufai.

El-Rufai ya fara shirin zaɓen 2027

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa ya miƙa takardar murbus ga shugabannin APC a mazaɓarsa da ke jihar Kaduna yau Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.

El-Rufai ya ci gaba da cewa:

"Duk da wannan mataki, a matsayina na mamba a SDP, zan maida hankali wajen jawo hankalin shugabannin adawa da sauran masu fafutuka don mu haɗu a inuwar dimokuraɗiyya domin kalubalantar APC a duk zaɓuka da za a gudanar daga yanzu zuwa 2027, in sha Allah.
"Saboda haka, ina kira ga dukkan magoya bayanmu da duk wanda ya damu da makomar ƙasarmu su shigo jam’iyyar SDP, domin mu gina Najeriya ta zama abin alfahari ga al’ummar Afirka da dukkan baƙar fata.
"Nagode, Allah Ya albarkaci jam’iyyar SDP, Allah Ya albarkaci Tarayyar Najeriya."

Martanin ƴan Najeriya kan sauya shekar El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa ƴan Najeriya sun yi magan kan sauya sheƙar Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP, wasu da dama sun yi maraba da ci gaban.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

Tun a kwanakin baya ne dai aka fara raɗe-raɗin El-Rufai zai fice daga APC duba da yadda yake sukar jam'iyyar a bainar jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya kara wannan labarin ta hanyar sanya kalaman El-Rufai kai tsaye kan batun sauya shekarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262