Cikin APC Ya Kada Yayin da El-Rufai Ya Ziyarci Babbar Jam'iyyar Adawa a Najeriya

Cikin APC Ya Kada Yayin da El-Rufai Ya Ziyarci Babbar Jam'iyyar Adawa a Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar SDP ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba
  • Wata majiya mai tushe ta ce El-Rufai ya ziyarci shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa ne domin neman shawarwari
  • A wani faifan bidiyo da aka sanya a shafin X, an ji El-Rufai yana cewa ana iya saka hotunan a shafukan sada zumunta kuma bai damu da hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ziyarci shugabannin jam'iyyar adawa ta SDP.

Tsohon gwamnan ya kai wannan ziyarar ne, a ranar Laraba, 20 ga watan Maris yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewa yana shirin tattara ƴan komatsansa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Hotunan Ribadu da jiga-jigan APC sun ziyarci El-Rufai yayin da ake jita-jitar zai bar jami'yyar

El-Rufa'i ya ziyarci shugabannin jam'iyyar SDP
Nasir El-Rufa'i ya sa labule da shugabannin jam'iyyar SDP Hoto: @B_ELRUFAI
Asali: Twitter

Me ya sa El-Rufai ya ziyarci sakatariyar SDP?

Jaridar Nigerian Tribune ta ce wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, tsohon gwamnan ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar SDP ta ƙasa ne domin tuntuɓar shugabannin jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Shehu Musa Gabam.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban SDP na ƙasa ya bayyana El-Rufa’i a matsayin makusancinsa mai tasiri a siyasa, ya ƙara da cewa ana buƙatar shugaba mai kawo sauyi irinsa.

Gabam ya godewa tsohon gwamnan jihar ta Kaduna da muƙarrabansa kan ziyarar.

Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ajiye bambancin addini, siyasa, da ƙabilanci domin ciyar da ƙasar nan gaba.

Shin El-Rufai ya fice daga APC?

Sai dai, a wani faifan bidiyo da tashar AIT ta wallafa a shafinta na X, a safiyar ranar Alhamis, ta ce gwamnan ya ziyarci sakatariyar ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa wata jam'iyya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fadi abin da ya kamata al'ummar jihar su yi domin kawo karshen 'yan bindiga

A lokacin da ake ɗaukar bidiyon, wani ya gaya wa mai ɗaukar hoton kada ya sanya shi a shafin X, amma an ji El-Rufai yana cewa, “A bari su ɗora, ban damu ba."

El-Rufai ya ba Bello kuɗin kamfe

A wani labarin kuma, kun ji cewa Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Ƙaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i, ya faɗi kuɗin da mahaifinsa ya ba shi lokacin da yake yin takara.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa N5m, El-Rufai ya ɗauko ya ba shi lokacin da yake yin yaƙin neman zaɓe a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel