Majalisar Dattawa Ta Hana Katsina da Wasu Jihohin Najeriya Yin Sulhu da 'Yan Bindiga

Majalisar Dattawa Ta Hana Katsina da Wasu Jihohin Najeriya Yin Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatocin jihohi su daina kulla yarjejeniyar sulhu da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane
  • Sanatoci sun ce irin wadannan yarjejeniyoyi ba sa kawo zaman lafiya mai dorewa kuma kan taimaka wa masu laifi da kudade
  • Majalisar ta umarci 'yan sanda da cibiyar tsaro ta yanar gizo su kamo 'yan bindigar da ke amfani da TikTok wajen nuna dukiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatocin jihohi a fadin Najeriya da su dakatar da tattaunawa da yarjejeniyoyin sulhu da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.

Sanatocin sun bayyana cewa irin wadannan matakai galibi ba sa samar da mafita mai dorewa, sannan suna iya zama hanyar da ke kara karfafa ayyukan ta'addanci ta hanyar samar wa masu laifi kudade.

Kara karanta wannan

Abu ya kai makura, majalisa ta bukaci cafke ƴan bindiga da ke wasa da kuɗi a TikTok

Majalisa.
Sanatoci suna tsakiyar zama a zauren Majalisar dattawa da ke Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Daily Trust ta kawo rahoton cewa majalisar ta kuma umarci Rundunar 'Yan Sanda da Cibiyar Kula da Tsaron Intanet su bibiyi tare da cafke masu garkuwa da mutane da 'yan bindigar da ke amfani da kafafen sada zumunta, musamman TikTok.

Sanatocin sun nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin masu aikata laifin ta'addanci ke bayyana a bidiyo suna nuna tarin kudade da ake zargin sun samu ne daga ayyukan garkuwa da mutane.

Harin Kogi ya tada hankalin majalisa

Wadannan matakai sun biyo bayan kudirin da Sanata Sunday Karimi ya gabatar kan sababbin hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a yankin Kogi ta Yamma.

A cewarsa, kwanan nan wasu 'yan ta'adda sun kai hari makarantar sakandare da ke Iluke-Bunu a karamar hukumar Kabba/Bunu, inda suka yi yunkurin sace daliban da ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta SSCE.

Sanata Karimi ya ce harin ya yi sanadin mutuwar mataimakin shugaban makarantar, wani malami da kuma wani mazaunin yankin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Musulmai sun yi martani da ake alakanta addinin da ta'addanci da sace mutane

Sanatan ya kuma bayyana cewa lamarin ya faru ne kwana guda bayan wani makamancin hari da aka kai wani gida a Odo-Ere da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma a ranar 8 ga Yunin 2026.

An gayyaci jami'in kula da makamai

Bayan tattaunawar, majalisar ta gayyaci shugaban Cibiyar Kula da Kanana da Matsakaitan Makamai ta Kasa domin ya yi wa sanatoci bayani kan matsalar yawaitar makamai a Najeriya da kuma matakan da ake dauka domin magance ta.

Sanatocin sun nuna damuwa cewa yawaitar makamai na daga cikin manyan abubuwan da ke kara ta'azzara matsalar tsaro a sassa daban-daban na kasar nan.

Majalisa.
Yadda sanatoci ke gudanar da zama a zauren Majalisar dattawa da ke Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Majalisa na son daina shigo da tufafi

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta nemi a hana shigo da tufafi daga waje domin farfado da masana’antar masaku tare da samar da ayyukan yi a Najeriya.

Majalisar ta kuma bukaci hukumar Kwastam ta Najeriya da ta kara tsaurara tsaro a dukkan iyakokin kasar domin dakile ayyukan fasa-kwaurin shigo da tufafin.

Haka kuma ‘yan majalisar sun yi kira ga gwamnati da ta ba da muhimmanci ga noman auduga, kasancewar shi ne muhimmin sinadari da ake bukata wajen farfado da masana’antu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262