Tirkashi: Hukumar Hisbah Kano Ta Haramta Sauraron Sabuwar Wakar Hamisu Breaker

Tirkashi: Hukumar Hisbah Kano Ta Haramta Sauraron Sabuwar Wakar Hamisu Breaker

  • Hukumar Hisbah ta Kano ta haramta sauraron wakar Amanata ta Hamisu Breaker, tana cewa wakar na yada alfasha da kalaman batsa
  • Ana zargin bidiyon da jarumar Kannywood, Khadija Mai Numfashi ta yi tana na rangaji da lumshe idanu a kan wakar ya janwo fushin Hisbah
  • Wasu na ganin matakin Hisbah talla ne ga Hamisu Breaker, suna cewa mutane da dama sun fara neman wakar ne bayan an hana ta sauraronta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitaccen mawakin soyayya, Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakar da ta jawo ce-ce-ku-ce, har ta kai ga hukumar Hisbah ta hana sauraronta.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta gargadi al'umma, musamman mata, da su guji sauraron wakar Hamisu Breaker mai taken 'Amanata.

Hukumar Hisbah ta Kano ta haramta sauraron wakar 'Amanata' ta Hamisu Breaker
Daga hagu zuwa dama: Sheikh Aminu Daurawa, Abba El-Mustapha, Hamisu Breaker. Hoto: Hamisu Breaker Dorayi, Hisbah Board Kano
Asali: Facebook

Hisbah ta hana sauraron wakar Hamisu Breaker

Gidan rediyon Dala FM da ke Kano ya fitar da wannan labarin a ranar Alhamis, ya rahoto cewa Hisbah ta ce wakar na dauke da kalaman badala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton gidan rediyon ya nuna cewa:

"Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kira ga matasa da su ƙauracewa sauraron waƙar Amanata ta Hamisu Breaker, tana mai cewar wannan waƙar haramun ce baki ɗaya.
"Mataimakiyar babban kwamandan Hisbah a ɓangaren mata, Dakta Khadija Sagir Sulaiman ce ta bayyana hakan, ta ce, waƙar ta fito ƙarara tana nuna zina daga yadda mata suke hawa suna irin wani lanƙwashe-lanƙwashe da karya murya."

Me ya sa aka hana sauraron wakar Breaker?

A binciken da Legit Hausa ta yi, an gano cewa mata, musamman jaruman Kannywood da kuma wadanda suka yi shuhura a TikTok, su ne suka jawo wakar ta bazu ko ina.

An ga wasu matan Kannywood, kamar Khadija Mai Numfashi, Momee Gombe suna rangaji da lumshe idanuwa yayin da suke bin wakar 'Amanata' ta Hamisu Breaker.

Bidiyon da Mai Numfashi ta yi ne ya fi jan hankali, wanda har wasu ke ganin shi ne ma babban dalilin da ya sa Hisbah ta hana sauraron wakar, don kar sauran mata su kwaikwayi jarumar.

A cikin bidiyon na Khadija Mai Numfashi, an ga yadda take lumshe idanuwa, tana rangaji da jiki da kanta, tana yin wani irin salo da ake ganin ya fi kama da 'badala.'

Kalli bidiyon da Mainumfashi ta yi a kasa:

Me Hamisu Breaker ke cewa a cikin wakar?

Mutane da yawa na mamakin dalilin Hisbah na hana sauraron wannan waka ta Hamisu Breaker, domin wasu na ganin wakar ba ta dauke da kalaman batsa.

Ya'u Shareef daga jihar Kaduna, ya shaida wa Legit Hausa cewa Hamisu Breaker ya yi kaurin sunan da wakokinsa na tasiri ga dabi'un mutane, musamman mata 'yan TikTok.

"Mata a TikTok kamar jira suke yi ace Breaker ya yi waka, za ka ga suna hawan wakar a shafukansu. To balle wannan da ya canja salon yadda yake wake.

"Sai dai fa, abin da Hisbah ta yi ne zai kara jan ra'ayin mutane kan wakar, domin na tabbatar akwai mutane da yawa da ba su san ya saki wakar ba.
"Idan ka lura, kwana biyu ya yi sanyi, ba kasafai za ka ji wakokinsa na tashe ba, amma ina tabbatar maka, wannan wakar za ta sake sa wa ya yi tashe."

- Ya'u Shareef.

Bashir Liyafa Abdurrazzak, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya saurari wakar 'Amanata,' amma bai ga dalilin Hisbah na hana sauraron wakar ba.

Ya yi kokarin rubuta wakar gaba dayanta, inda muka dauko bangare daya da matan suka fi rerawa kamar haka:

"Mai kishina ina sonki
"Mai zan baki na aure ki?
"Son ki yana ta ginan ɗaki
"Mu yi zamanmu a tare dake ciki
"A cikin ciki can ciki."
Mutane sun yi martani da Hisbah ta haramta sauraron wakar Hamisu Breaker
Mawaki Hamisu Breaker. Hoto: Hamisu Breaker Dorayi
Asali: Twitter

Me mutane ke cewa kan matakin Hisbah?

Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin mutane kan matakin da Hisbah ta dauka na hana sauraron wakar Hamisu Breaker:

Omar Fagge:

"Yanzu Hisbah za su sa a yi ta neman wakar don a ji dalili. Hukumar tace fina finai ne da wannan aikin. Gwamnatin Kano fa sai sun yi taron karawa juna sani kan ayyukan hukumomi."

Aliyu Hydar:

"Yanzu wadanda basu santa ba kuma zasu tafi neman ta."

HAUSA 210:

"Wannan ai talla kuka yi masa, ni ma wallahi ban san wakar ba sai da ku ka fada yanzu na ji, ka ga kenan za aje a nemi sunan wakar a intanet. Allah ya kyauta."

Nasser Ya'u Zara:

"Talla kyuta. Wallahi yada barna kamar taimako ne a kan barna. In ban da yau ban taba jin sunan wakar ba."

Meenal Umar:

"Nima ban san ta ba amma sai na nemo na ji me ake cewa wallahi."

Alakar Momee Gombe da Hamisu Breaker

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitacciyar jarumar Kannywood, Momee Gombe, ta musanta zargin soyayya da mawaki Hamisu Breaker.

A wata hira da Hadiza Gabon, Momee Gombe ta ce mutane ne kawai ke ƙirƙirar soyayya tsakaninsu da Breaker a zuciyarsu ba tare da hujja ba.

Ta jaddada cewa babu soyayya tsakaninsu, Breaker kawai abokin aikinta ne, kuma suna da kyakkyawar fahimta da mutunta juna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.