"Abokin Sana'a Na Ne", Momee Gombe Ta Ce Ba Ta Taɓa Soyayya Da Hamisu Breaker Ba

"Abokin Sana'a Na Ne", Momee Gombe Ta Ce Ba Ta Taɓa Soyayya Da Hamisu Breaker Ba

  • Fitacciyar jarumar fim ɗin Kannywood Momee Gombe ta ce ba ta taɓa soyayya da Hamisu Breaker ba
  • Momee Gombe ta ce mutane ne kawai suke irin wannan tunanin saboda ganin suna mu'amala tare
  • Jarumar wacce haifaffiyar Gombe ce, ta kuma bayyana yadda ta tsinci kanta a masana'antar Kannywood

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Fitacciyar jarumar Kannywood Maimunatu Abubakar wacce aka fi sani da Momee Gombe, ta bayyana cewa babu soyayya tsakaninta da Hamisu Breaker.

Ta bayyana hakan ne a hirarta da jaruma Hadiza Gabon cikin shahararren shirin nan na ta 'Gabon's Room Talk Show' da take gabatarwa a YouTube.

Momee Gombe ta ce babu soyayya tsakaninta da Hamisu Breaker
Momee Gombe ta ce Hamisu Breaker abokin sana'arta ne kawai babu alaka ta soyayya tsakaninsu. Hoto: Momee_Gombe
Asali: Instagram

Momee Gombe ta ce Hamisu Breaker abokin sana'arta ne kawai

Da take amsa tambayar da Gabon ta yi mata kan ko akwai soyayya tsakaninta da mawaƙi Hamisu Breaker, Momee Gombe ta bayyana cewa mutane ne kawai ke tunanin hakan a ransu.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Wata Likita Bayan Yin Basaja A Matsayin Marasa Lafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalaman Momee Gombe:

“Da zarar mutane sun ga kana mu'amala da mutum sai su ɗauka soyayya ce, amma maganar gaskiya ni ban taɓa soyayya da shi ba.”

Ta ce babu wani abu na soyayya da ke tsakinta da Breaker, illa iyaka abokin sana'arta ne kuma suna da kyakkyawar fahimta a tsakaninsu.

Yadda ta shigo masana'antar Kannywood

Momee Gombe ta bayyana cewa babban mai shirya finafinai Usman Muazu wanda shi ma ɗan asalin Gombe ne ya yi silar shigowarta fim.

A cewarta Usman ya kasance kamar ɗan gida ne a gidan nasu, domin kuwa yana shiga ko ina kuma kowa dake gidan ya san shi.

Ta bayyana cewa ta kasance tana yawan tambayarsa kan cewa tana so ta shiga harkar fim a duk lokacin da suka zo ɗaukar fim a Gombe.

Sai dai a cewar Momee, Usman ya kan ce mata ba za a barta a gida ba, amma daga bisani kuma aka barta ta fara harkar fim ɗin.

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Allah Ya Yi Wa Fitacciyar Jarumar Shirin Fim a Najeriya Rasuwa

Kalli cikakkiyar hirar a ƙasa:

Abba El-Mustapha ya ce 'yan Kannywood za su dara a gwamnatin Abba Gida Gida

Legit.ng a kwanakin baya ta kawo muku rahoto kan bayanin da jarumin Kannywood Abba El-Mustapha ya yi na cewa gwamnatin jihar Kano mai ci ta Abba Gida Gida za ta taimaki masana'antar Kannywood.

Ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan rediyon Freedom, inda ya ba da tabbacin cewa 'yan fim za su dara gwamnatin ta Abba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel