Buhari Ya Bi Sahun Masu Makokin Fafaroma, Ya Tunawa Duniya Hudubar da Ya Bari

Buhari Ya Bi Sahun Masu Makokin Fafaroma, Ya Tunawa Duniya Hudubar da Ya Bari

  • Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rasuwar Fafaroma Francis a matsayin babban rashi ga Kiristocin duniya
  • Buhari ya kara da cewa duniya ba za ta manta da irin jagorancin da Fafaroma ya nuna ba, wanda ya haɗa da gaskiya, adalci da kula da talakawa
  • Ya jinjinawa Fafaroma Francis saboda yadda ya ba da muhimmanci ga rayuwar marasa galihu, masu bukata ta musamman da ‘yan gudun hijira
  • Tsohon shugaban ya ce yana fatan Isra’ila da Hamas za su saurari kiran Fafaroma na kawo karshen rikicin da ake yi a Gaza don girmama mamacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa Kiristoci a Najeriya da ma duniya baki ɗaya za su yi kewar irin jagorancin ƙwarai na Fafaroma Francis.

A safiyar Litinin, Fadar Vatican ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis yana da shekaru 88, inda ta bayyana cewa ya rasu sakamakon matsanancin ciwon zuciya.

Fafaroma
Buhari ya yi jimamin rasuwar Fafaroma Francis Hoto: Pope Francis/Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, hadimin Buhari na musamman, ya fitar, wadda aka wallafa a shafin Facebook na tsohon shugaban kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya jinjinawa Fafaroma Francis

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Buhari ya bayyana Fafaroma Francis a matsayin shugaba mai sadaukarwa, wanda ya yi rayuwarsa wajen hidima ga talakawa da mabukata.

A cewarsa:

“Fafaroma ne wanda ya dage wajen gina kyakkyawar alaka tsakanin mabiyan manyan addinai biyu na duniya — Musulunci da Kiristanci."

Buhari ya kara da cewa:

“Kafin rasuwarsa, Fafaroma Francis ya yi kiran a kawo karshen yaki a Gaza, wanda ya nuna jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya a duniya."

Buhari ya nanata sakon Fafaroma

Tsohon shugaban kasan ya bayyana fatan cewa Isra’ila da Hamas za su saurari kiran da Fafaroma ya yi, a matsayin girmamawa na ƙarshe ga rayuwarsa da kokarinsa na wanzar da zaman lafiya.

Buhari
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Muhammadu Buhari ya ce:

“Ina fata Isra’ila da Hamas za su saurari wannan kira a matsayin girmamawa ta ƙarshe ga Fafaroma Francis, wanda ya shahara wajen kawo batun sauyin yanayi zuwa Vatican, tare da amincewa da a samar da ƙasar Falasdinu,."

Ya kara da fatan cewa za a zabi sabon jagoran cocin Katolika wanda zai ci gaba daga inda Fafaroma Francis ya tsaya, musamman wajen ciyar da duniya gaba da koyarwar jin ƙai da adalci.

Abin da zai faru bayan mutuwar Fafaroma

A baya, mun wallafa cewa fadar Vatican ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis ya na da shekaru 88 biyo bayan rashin lafiya, bayan ya shafe shekaru 12 yana jagorantar cocin Katolika na duniya.

Marigayi Francis, wanda ya shahara da koyi da Yesu Almasihu da kokarinsa na hada kan addinai, ya rasu ne sakamakon bugun jini a kwakwalwa da kuma ciwon zuciya, in ji Vatican.

Biyo bayan rasuwarsa, an fara aiwatar da tsarin da ake bi tun ƙarni da dama wajen zaɓen sabon Fafaroma, inda Kadinoli daga sassa daban-daban na duniya za su taru a Vatican don taron sirri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.