Rawar Solo: Jaruma Khadija Mai Numfashi Ta Nemi Afuwar Hukumar Tace Fina-Finai Bayan Dakatar da Ita

Rawar Solo: Jaruma Khadija Mai Numfashi Ta Nemi Afuwar Hukumar Tace Fina-Finai Bayan Dakatar da Ita

  • Jaruma Khadija Mai Numfashi ta nemi afuwar hukumar tace fina-finai da masana'antar Kannywood
  • Wannan ya biyo bayan dakatar da ita da shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha ya yi na tsawon shekaru da biyu
  • An haramtawa jarumar shiga duk wasu harkokin masana'antar sakamakon billar wani bidiyon rawan da ta yi a gidan gala wanda ya haddasa cece-kuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Khadija Kabir Ahmad, wacce aka fi sani da Khadija Mai Numfashi, ta yi martani bayan dakatar da ita da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yi.

Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba Al-Mustapha ya sanar da haramtawa jarumar shiga duk harkokin masana’antar, bayan an dakatar da ita na tsawon shekaru biyu.

Kara karanta wannan

"Ina son mahaifinsa idan yana raye don Allah": Matashiya ta fadi dalilinta na auren tsoho

Khadija ta ba da hakuri
Rawar Solo: Jaruma Khadija Mai Numfashi Ta Nemi Afuwar Hukumar Tace Fina-Finai Bayan Dakatar da Ita Hoto: Khadija Mai Numfashi
Asali: Facebook

An dakatar da jarumar ne akan wani bidiyon rawar Solo da ta yi a wani gidan Gala, wanda ya haddasa cece-kuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, Mai Numfashi ta nemi yafiyar hukumar da daukacin jama’ar da bidiyon bai yi wa dadi ba, inda ta ce ita kanta ba ta ji dadin abun da ta aikata a bidiyon ba.

Jarumar ta ce:

“Ina kara ba hukumar tace fina-finai hakuri sannan ina kara ba wa masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood hakuri da daukaci al’ummar Annabi Muhammadu S.A.W gabaki daya wadanda basu ji dadin bidiyon ba. Ni kaina ban ji dadin bidiyon ba, ban ji dadin shi ba ina mai kara baku hakuri, ayi hakuri in shaa Allahu hakan ba zai kara faruwa ba. Nagode sosai."

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Ga bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani kan yafiyar da jarumar ta nema

Muhammad ishaQ y ace:

“za ki yi bayani ki ji babu dadi ”

Aisha Najamu ta ce:

“Allah ya shiryamu baki daya yacanza mana mummunan kaddarar mu izuwa kyakykyawan kaddara sis✊✊”

Maryam uzairu nadabo ta ce:

“naji dadi dakikafito kikabada hakuri,Allah yakara kiyaye gaba.”

Khaleepha_chairman_27

"Wow wallahi kin kyauta sosai ❤️❤️

user3346513325345 ya ce:

“Wlh sai kika qara birgeni Allah ya kiyaye nagaba.”

Baiwar Allah ta ce:

“Allah srk my queen wannan shine halin musulmi nakwarai yakarba kuskurenshi alokachinda akasanardashi sannan yagyara Allah yasamudache munyafemike ”

Legit Hausa ta tuntubi jarumar ta dandalinta na Instagram don jin ta bakinta amma bata amsa ba har zuwa yanzu.

Jarumi zai ba Abba rikon yaransa

A wani labarin kuma, mun ji cewa Abdul Haseer wanda ya shahara da suna Malam Ali a shirin Kwana casa’in, ya koka game da dakatar da shi da aka yi daga harkar fim.

A bidiyon da Abdul Haseer ya fitar a dandalin sada zumunta wanda mu ka ci karo da shi a Twitter, ya aikawa Gwamna Abba Kabir Yusuf sako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel