Alaka Ta Yi Tsami, Atiku Ya Yi Wa Obasanjo Sabon Tonon Silili
- Atiku Abubakar ya ce ya tsaya tsayin daka wajen taimaka wa Olusegun Obasanjo a lokacin da yake gidan yari
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya ciyar da Obasanjo tare da tufatar da shi bayan ya samu ’yanci daga gidan yari
- Atiku ya danganta sabuwar sukar da Obasanjo ya yi masa da rashin jin dadinsa kan gazawar shirinaa na yin wa’adi na uku a mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce ya ciyar da Olusegun Obasanjo tare da tufatar da shi bayan ya fito daga gidan yari.
Atiku ya ce a lokacin da Obasanjo ya samu ’yanci, ba shi da wani abu mai yawa, don haka ya karbe shi tare da tabbatar da cewa an kula da shi yadda ya kamata kuma bai rasa komai ba.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026.
Hakan na zuwa ne bayan Obasanjo ya bayyana cewa daya daga cikin manyan nadamarsa a rayuwa shi ne daukar Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Sai dai Atiku ya ce sabuwar sukar da Obasanjo ya yi masa ta samo asali ne daga rashin jin dadinsa kan gazawar shirin neman wa’adi na uku da ake alakanta shi da shi shekaru da suka gabata.
Atiku ya tuna halascinsa ga Obasanjo
Atiku Abubakar ya ce ya kalli hirar da Obasanjo ya yi kwanan nan cikin alhini maimakon fushi.
Da yake tuna tarihinsu, Atiku ya ce ya tsaya tare da tsohon shugaban kasar a lokacin da yake gidan yari, tare da taimaka wa iyalansa.
Ya ce ya kuma yi aiki tare da wasu ’yan kasa masu kishin kasa domin ganin an saki Obasanjo, kafin daga baya ya taimaka wajen gina kawancen siyasar da ya kai shi ga zama shugaban kasa.
“Tarihi ya nuna cewa a lokacin da Cif Obasanjo yake gidan yari, na tsaya tsayin daka tare da shi. Na taimaka wa iyalansa, na yi aiki ba tare da gajiyawa ba tare da wasu ’yan kasa masu kishin kasa domin a sake shi, kuma ban taba daina yarda cewa ya cancanci samun ’yancinsa ba.”
- Atiku Abubakar
Abin da Atiku ya ce kan Obasanjo
Atiku ya ce bayan Obasanjo ya samu ’yanci, ya same shi cikin yanayin da ba shi da wani abu mai yawa
“Lokacin da daga bisani ya samu ’yancinsa, ba shi da wani abu mai yawa. Na karbe shi, na tufatar da shi, na tabbatar an kula da shi yadda ya kamata, sannan na ba shi dukkan taimakon da ya dace domin ya sake tsayawa da kafafunsa.”
- Atiku Abubakar
A baya-bayan nan, Obasanjo ya bayyana cewa babban nadamarsa a rayuwa shi ne daukar Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Source: Twitter
Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamanti kan sayo motocin alfarama 39.
Atiku ya bukaci gwamnatin Shugaba Tinubu ta fito fili ta bayyana cikakkun bayanai kan shirin sayen motocin alfarma 39 da aka ware kuɗinsu Naira biliyan 15.13 a kasafin kuɗin shekarar 2026.
Asali: Legit.ng

