Alkawarin da Shugaba Tinubu Ya Yi ga Yan Najeriya game da Addininsu
- Shugaba Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare 'yancin addini kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada
- Tinubu ya yabawa ƙungiyar Ansar-Ud-Deen saboda gudunmawar da ta bayar tsawon sama da shekara ɗari a ilimi, lafiya, addini
- Mataimakin gwamnan Legas da shugabannin ADSN sun buƙaci ci gaba da inganta ilimi, tarbiyya da haɗin gwiwa domin gina Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare 'yancin addini a kasar.
Tinubu ya ce zai yi hakan ne kamar yadda kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya tanada.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da sabon hedikwatar ƙungiyar Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria mai suna Hassanat Abebi Okunnu House da ke Surulere a Legas, cewar The Nation.
Alkawarin da Tinubu ya yi ga yan Najeriya
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya wakilce shi a taron da aka yi.
Ya ce gwamnati za ta kuma ƙarfafa ƙungiyoyin addini su bunƙasa haƙuri da zaman lafiya da kuma adalci.
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da 'yancin addini tare da ƙarfafa ƙungiyoyin addini su inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna domin ci gaban Najeriya.
Tinubu ya yabawa ƙungiyar Ansar-Ud-Deen saboda irin gudunmawar da ta bayar fiye da shekara ɗari a fannoni kamar ilimi, tarbiyya, harkokin addini, kiwon lafiya, ayyukan jin ƙai da ci gaban al'umma.
Ya bayyana cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya gina Najeriya da ake buri ba, yana mai cewa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin addini masu kyawawan manufofi yana da matuƙar muhimmanci wajen gina al'umma mai ilimi da ɗabi'a.

Source: Facebook
Yabon da Tinubu ya yi ga ƙungiyar Ansar-Ud-Deen
Shugaban ya kuma yabawa Alhaji Femi Okunnu, wanda ya bayar da ginin hedikwatar, saboda sanya masa sunan mahaifiyarsa marigayiya Hassanat Abebi Okunnu.
Mataimakin gwamnan Legas, Dakta Kadiri Hamzat, ya buƙaci ƙungiyar ta ci gaba da riƙe manufofinta na bunƙasa ilimi, tarbiyya da ɗa'a. Ya ce ta taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa ilimin zamani tsakanin Musulmai.
Shugaban ƙasa na Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria, Alhaji Mosediq Adeniji Kazeem (SAN), ya ce sabon hedikwatar alama ce ta sabon ƙuduri wajen ƙarfafa addini, ilimi da ci gaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da zuba jari wajen bunƙasa matasa da ƙarfafa cibiyoyinta, cewar rahoton Daily Post.
Dattawan Kiristoci sun soki salon mulkin Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Kungiyar dattawan Kiristoci ta kasa ta ce gwamnatin Bola Tinubu ta gaza a bangaren tsaro, tattalin arziki da walwalar jama'a.
Dattawan sun bukaci shugaban kasar ya hakura da neman wa'adi na biyu, ya mayar da hankali kan sake fasalin Najeriya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da bangaren shari'a su tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin adalci.
Asali: Legit.ng

