"Ba Mu Buƙatar Albarkar Shi kafin Fatattakar Tinubu," Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari

"Ba Mu Buƙatar Albarkar Shi kafin Fatattakar Tinubu," Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya soki gwamnatin Bola Tinubu, yana cewa ta na jefa talakawa cikin yunwa
  • Ya kara da cewa wannan babban dalili ne da zai sa kuma ‘yan siyasa masu kishin kasa za su nemi kifar da gwamnatin APC a 2027
  • Kan batun shiga hadakar jam'iyyu, Babachir Lawal ya ce ba su bukatar amincewar tsohon shugaban ƙasa watau Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya nuna damuwa matuƙa kan yadda al’amura ke gudana a Najeriya a halin yanzu. Babachir ya kuma ce waɗanda ke ƙoƙarin samun goyon bayan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ciki har da magoya bayan Shugaba Bola Tinubu, na bata lokacinsu.

Tinubu
Babachir Lawal ya soki gwamnatin Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ya fadi haka a wata hira da ta kebanta ga jaridar Punch, inda ya dage cewa duk wani jigon CPC da ke da kishin talakawa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen korar kowace gwamnati da ke jefa jama’a cikin wahala ba.

Tsagin CPC a jam'iyyar APC ya soki Tinubu

Babachir Lawal ya ce duk ɗan siyasar da ke da tunani mai kyau dole ne ya kifar da gwamnati irin ta Tinubu da ke jefa mutane cikin talauci nan da 2027. Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Waɗannan mutane sun ba mu hujja ta fito-na-fito da su domin CPC gungun talakawa ne. Gungu ne da ke da kishin jin daɗin ƙasa da ɓangarorin da aka danne. Wannan shi ne akidarmu, wanda muka koya daga Buhari.
''Babban burinmu shi ne mu yi wa waɗanda aka hana ‘yancinsu da wanda aka nuna wa wariya a cikin al’umma hidima. Amma wannan gwamnati ta mai da wahala da wariya kamar addini.'

Babachir: 'Tsagin CPC na jin zafin mulkin Tinubu'

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce, halin da Najeriya ke ciki yanzu na taɓa zuciyar duk 'yan CPC na hakika

Haka kuma hakan zai tursasa masu ɗaukar mataki ba tare da wata-wata ba domin kifar da wannan tsarin da ke ci da gumin marasa ƙarfi a cikin al’umma.

Buhari
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Babachir Lawal ya ce:

“Wannan shi ne abin da Buhari ya tsaya a kai. Wannan shi ne abin da muka koya daga gare shi.”
“Da farko, ba ma bukatar amincewar Buhari. Abin da muke bukata kawai shi ne mu gaya masa abin da muke shirin yi, domin duk manya ne mu.'

Ana kokarin jawo Buhari daga APC?

Babachir Lawal ya bayyana cewa ba su da niyyar gayyatar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa tafiyarsu.

Ya ce;

'Ko da Buhari ya ce, ‘Ku saurara, zan biyo ku.’ To, namu ne mu ce, ‘A’a, Oga, don Allah ka tsaya a gefe. Ka fi ƙarfinmu. Ba ma son mu haɗa da kai. Ka riga ka zama ɓangare na wannan gwamnati. Don Allah ka ci gaba da kasancewa a can har sai ka gaji.”

Babachir Lawal, wanda ya kasance ɗaya daga cikin wadanda suka kafa CPC kuma tsohon abokin tafiyar Tinubu ne, yanzu haka yana daga cikin manyan sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa.

Abin da APC ta shirya wa Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa alamu na nuna cewa jam’iyyar APC na iya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu tikitin takarar shugaban ƙasa kai tsaye ba tare da adawa ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa ƙarfi da ƙarfe don fuskantar Bola Tinubu a babban zaɓen da ke tafe da niyyar kifar da gwamnati.

Wasu daga cikin waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu sun ce shugabannin jam’iyyar na ganin cewa Tinubu ya cancanci tazarce kuma ba za a kalubalance shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.