Trump Ya Ja da Baya kan Kai Munanan Hare Hare kan Iran, an Ji Dalili

Trump Ya Ja da Baya kan Kai Munanan Hare Hare kan Iran, an Ji Dalili

  • Shugaba Donald Trump ya ce ya janye shirin kai hari kan Iran muddin za a iya cimma yarjejeniya cikin gaggawa
  • Donald Trump ya ce Iran da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya sun bukaci Amurka ta dakatar da kai harin
  • Rahotanni sun ce Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya nuna damuwa kan shirin kara kai hare-hare kan Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya janye shirin kai hari kan Iran bisa sharadin cewa za a iya cimma yarjejeniya cikin gaggawa.

Trump ya ce Iran da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya sun bukaci Amurka ta dakatar da kai hare-hare, yana mai cewa an riga an cimma matsaya kan muhimman sharuddan yarjejeniyar.

Trump ya fasa kai hari a Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump Hoto: @Drpezeshkian, @DonaldJTrump
Source: Twitter

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Lahadi, 2 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami, Atiku ya yi wa Obasanjo sabon tonon silili

Ya ce yarjejeniyar za ta hada da bude mashigar Hormuz baki daya cikin gaggawa tare da kawo karshen barazanar shirin nukiliyar Iran.

Trump ya bayyana matsayar Amurka

Trump ya ce Amurka ta shirya tsaf domin daukar matakin soji kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da karfin da ba a gani ba tun bayan yakin duniya na biyu.

“Amurka ta shirya tsaf kuma tana cikin shirin kai hari kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da matakin karfin soja da iko da ba a taba gani ba tun bayan yakin duniya na biyu.”

- Shugaba Donald Trump

Trump ya ce duk da wannan shiri, Iran da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya sun bukaci a dakatar da kai harin saboda an amince da muhimman sharuddan yarjejeniya.

Ya kara da cewa:

“Wannan zai hada da bude mashigar Hormuz cikin gaggawa, baki daya kuma ba tare da wani sharadi ba, tare da kawo karshen barazanar nukiliyar Iran.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Iran ta jawo matsala da Trump ya yi sabuwar barazana

Trump ya janye shirin kai hari

Trump ya ce ya amince da janye harin domin amfanin duniya da kuma tabbatar da makomar Iran mai nasara da wadata.

“Bisa wannan bukata, na amince da janye harin domin amfanin duniya a nan gaba, tare da tabbatar da ci gaban Iran mai nasara da wadata, bisa sharadin cewa za a iya cimma yarjejeniya cikin gaggawa.”

Shugaban Amurka ya ce kasar Isra’ila ma ta amince da wannan matsaya.

“Kowa ya fara aiki, a tabbatar an kammala yarjejeniyar.”

- Shugaba Donald Trump

Trump ya fasa kai hari kan Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yariman Saudiyya ya yi magana

Rahotannin kafafen yada labarai na Amurka sun ce Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya tattauna da Trump ta waya a ranar Asabar.

Rahotannin Axios da kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) sun ce yariman ya nuna damuwa kan shirin kara kai hare-hare kan Iran.

Axios, yana mai nakalto wani jami’in Amurka, ya ce Yarima Mohammed ya bayyana damuwarsa tare da neman karin bayani kan shirin daukar matakin.

Kara karanta wannan

An cimma matsaya da Hamas, Trump zai fatattaki Isra'ila a Gaza

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta ce yariman ya bukaci Trump ya rage tashin hankali tare da kauce wa kaddamar da hare-haren.

Iran ta lalata jiragen yakin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi ikirarin lalata jiragen yaƙin F-35 guda uku na Amurka.

Rundunar IRGC ta kuma bayyana cewa ta yi wa wasu jiragen guda uku mummunar ɓarna a wani hari da ta kai sansanin sojojin sama na al-Azraq da ke kasar Jordan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng