Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske

Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske

A cikin kwanakin shagalin bikin sallah karama ne wani sabon al'amari ya ziyarci yankin arewacin Najeriya.

An ga bidiyon matan aure daban-daban suna cashewa a gaban mazansu, lamarin da ya jawo cece-kuce daga jama'ar da suka hada da malamai, 'yan mata, samari da sauransu.

A yayin da wasu sassa na jama'a ke bayyana cewa matan auren sun yi matukar birgesu, wasu na tofin Alla-wadai garesu na fallasa sirrin zamantakewa tare da nishadinsu a kafafen sada zumunta.

BBC ta samu zantawa da mawakin wakar "Jarumar Mata" a shafinsa na Instagram kai tsaye.

Duk da mawakin ya bayyana cewa ya saki wakar ne tun a karshen shekarar 2019 kuma har tayi tashe tare da lafawa, bai taba tsammanin za ta sake tashe kamar haka.

Kwatsam ya ga matan aure na tikar rawa a gaban mazansu tare da rangaji ga sautin wakarsa.

Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske
Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske. Hoto daga Arewamobile
Asali: Twitter

Ya ce, "Abinda yasa na yi wakar jarumar mata shine duba da yanayin mutane. Sau da yawa idan zan yi waka, ina duba halayyar mutane ne kamar su zurfafawa wajen soyayya.

"Hakazalika, na ga kwana biyu ban yi wa masoya waka ba, shiyasa nace bari in yi musu. Amma ba budurwata nayi wa ba."

Shaharren matashin mawakin ya bayyana cewa, tsaf ya zauna ya zabi kalaman da ya yi amfani da su a cikin wakar.

A misali na baitin farko 'Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciya ta ba...' wannan na bayyana cewa soyayyar ta har bayan rai ce mara sauyawa.

KU KARANTA: An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji

Matashin mawakin ya bayyana cewa, "Ban taba tsammanin wakar za ta zaburar da matan aure ba har su yi gasa a kanta ba. Na yi ta don masoya ne da fatan shahara amma sai ta yi farin jini na gaske."

Breaker ya ce, ya yi matukar jin dadin yadda wannan wakar ta sa ta bayyana gyaran aure da soyayya a arewa.

Ya ce bai san adadin mutanen da suka kira sa don sanar da shi yadda wakarsa ke tashe a kafafen sada zumuntar zamani ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel