Kosan Waka: An Fitar da Lokacin Jana'izar Fitaccen Mawakin Gwamnan Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana girman rashin da aka yi bayan an sanar da rasuwar fitaccen mawakin siyasa, Muhammadu Buhari
- An sanar da rasuwar mawakin da aka fi sani da Kosan Waka a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli, 2026 yana da shekara 47 bayan ya sha fama da rashin lafiya
- Gwamnan ya mika ta'aziyyarsa, yayin da aka sa lokacin jana'izar marigayin da za a yi a yau a ƙauyen Tsanni, ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar fitaccen mawakin siyasa, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, tare da mika ta'aziyya ga iyalansa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli, 2026.

Source: Facebook
Sanarwar da aka wallafa a shafin Facebook na Sanusi Bature ta bayyana cewa za a yi jana'izarsa a ƙauyen Tsanni da ke ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina da 5.00 na yammacin yau.
Gwamnan Kano ya yi alhinin Kosan Waka
Sanarwar ta kara da cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman mahaifiyarsa, tare da abokansa, abokan hulɗarsa, masoyansa da kuma daukacin al'ummar Jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana marigayin Kosan Waka a matsayin mai kishin ƙasa daga jihar Katsina da ya zauna a Kano, wanda waƙoƙinsa suka zarce siyasa, suka zama hanya mai ƙarfi ta inganta haɗin kai, al'adu da wayar da kan jama'a.
Ya kuma yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa kabari, Ya shigar da shi Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Ba za a manta da Kosan Waka ba - Gwamna
Marigayi Kosan Waka na daga cikin fitattun mawakan siyasa na Kano, inda hazakarsa, kirkirarsa da kuma salon gabatar da waƙoƙinsa suka sa ya samu karɓuwa a sassa daban-daban na Najeriya, a cewar sanarwar.

Source: Original
Gwamnatin ta ce za a ci gaba da tunawa da gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa sadarwar siyasa da kuma nishaɗi a fadin kasar nan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin Kano ta haɗa kai da masana'antar da miliyoyin masoyan marigayin a faɗin Najeriya wajen alhinin wannan rashi, tare da addu'ar Allah Ya sa ya huta.
Kano: Kosan Waka ya rasu
A baya, mun kawo labarin cewa fitaccen mawakin siyasa Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti da ke jihar Kano ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli, 2026.
Kosan Waka ya shahara da waƙoƙin siyasa, musamman waƙar "Abba ka cika gwarzo" da ya yi wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf wanda ya sa ya zama daya daga cikin fitattun mawakan siyasa a Arewacin Najeriya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai masa ziyara a asibiti domin duba lafiyarsa, lamarin da ya jawo hankalin jama'a yayin da ake ci gaba da yi masa addu'ar neman rahama da jin kan Allah SWT.
Asali: Legit.ng

