Amnesty International ta nemi Amurka ta cafke Benjamin Netanyahu yayin ziyararsa White House, yayin da aka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Amnesty International ta nemi Amurka ta cafke Benjamin Netanyahu yayin ziyararsa White House, yayin da aka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
'Yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude a birnin Abuja, yayin da matarsa, direbansa da jami'in tsaronsa suka jikkata. Ana ci gaba da bincike.
Sanata Shehu Sani ya ce yan Najeriya basa bukatar karanta littafin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin dai komai ya faru ne a kan idanunsu.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai kori Godwin Emefiele ba daga mukamin gwamnan CBN ba, saboda bai gaya masa zai yi takara ba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde,ya nemi amincewar majalisar dokokin jihar domin ciyo bashin Naira biliyan 150 daga cibiyoyin hada-hadar kudi na Afrexim da Access.
Rundunar sojin Najeriya ta fito fili ta yi magana kan jami'in sojan da ya bindige kansa har lahira a jihar Ogun. Rundunar ta ce harbin na kuskure ne.
Gwamnatin jihar Kano ta ware N8bn a gina firamare, kuma za a tanadi kayan aiki na zamani a makarantun karkara sannan ta ware kudi domin gyara sauran makarantu.
Hukumar NSCDC ta cafke wani mahaifi mai suna Chinana Talida a birnin Abuja a kokarin siyar da ɗan cikinsa mai shekaru shida a duniya kan kudi miliyan 20.
Wasu miyagun yan bindiga dauke da makamai sun kai sababbin hare-hare a wasu kauyuka guda biyu na jihar Neja. Yan bindigan sun sace mutane masu yawa.
Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutum 23 a kauyen Kawu da ke yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun tuntubi yan uwansu. Sun nemi kayan abinci da babura 5.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya shirya yakar matsalolin kwacen waya da kuma ta'ammali da miyagun kwayoyi da ya yi katutu a fadin jihar baki daya.
Labarai
Samu kari