Rundunar Sojin Najeriya Ta Bayyana Dalilin da Ya Sanya Jami'in Sojanta Ya Bindige Kansa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Bayyana Dalilin da Ya Sanya Jami'in Sojanta Ya Bindige Kansa

  • An ji dalili daga bakin rundunar sojin Najeriya kan jami'in sojanta wanda ya salwantar da ransa a jihar Ogun
  • Rundunar a cikin sanarwa ta bayyana cewa jami'in sojan ya bar duniya ne bayan ya harbi kansa a bisa kuskure
  • Rundunar ta musanta zargin da ake yi na cewa sojan ya yanke shawarar barin duniya ne saboda ba a biya shi kuɗin alawus ɗinsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan mutuwar ɗaya daga cikin jami'anta wanda ya harbe kansa har lahira a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Rundunar ta bayyana mutuwar jami'in sojan mai suna Boyi ThankGod, a matsayin wani lamari na harbi bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya bayyana abin da ya haddasa tashin abin fashewa a Ibadan, bidiyo ya bayyana

Rundunar soji ta fadi dalilin da ya sa jami'inta ya salwantar da ransa
Rundunar ta ce sojan ya yi harbin ne bisa kuskure Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Thanksgod, wanda ke aiki da barikin sojoji na Alamala, a Abeokuta, babban birnin jihar, ana zargin ya harbi kansa a kai lokacin da yake bakin aiki a ranar tunawa da sojoji, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani hoto mara kyawun gani wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta ya nuna gawarsa babu rai a kwance cikin jini, bayan da kansa ya rabu da jikinsa saboda harbin.

Me rundunar ta ce kan mutuwar sojan?

Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na runduna ta 81, Olabisi Ayeni, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ɗora alhakin harbin da sojan ya yi bisa kuskure.

A cewarsa, binciken musabbabin faruwar lamarin, ya nuna cewa, sojan da ya mutu, ya riƙe makaminsa ne cikin sakaci kuma ya yi harbi, wanda ya yi sanadin mutuwarsa, rahoton Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Abin bakin ciki yayin da sojan Najeriya ya bindige kansa, ya mutu cikin bariki, bayanai sun fito

Ayeni ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

Ya musanta zargin da ake yi na cewa sojan ya salwantar da ransa ne saboda rashin biyan kuɗaɗen alawus ɗinsa.

Wata Soja Ta Yi Sabuwar Fallasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata soja ta fito fili ta yi fallasa kan yadda wasu na sama da ita ke yi wa rayuwarta barazana.

Sojan a wasu bidiyoyi da ta sanya a TikTok ta bayyana cewa manyan sojojin na yi mata barazanar ne saboda ta ƙi yarda su yi lalata da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel