Amnesty na Neman a Cafke Netanyahu da Ya Je Amurka wajen Trump

Amnesty na Neman a Cafke Netanyahu da Ya Je Amurka wajen Trump

  • Kungiyar Amnesty International da ke Nigeria ta bukaci hukumomin Amurka su cafke Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, tare da gurfanar da shi
  • Masu goyon bayan Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga a gaban Fadar White House, suna sukar goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila a yakin Gaza
  • Wani rahoto ya nuna cewa sabon bahasin kuri'ar jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa kusan rabin Amurkawa na goyon bayan cafke Netanyahu da ya ziyarci kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington DC – Kungiyar Amnesty International ta Najeriya ta bukaci hukumomin Amurka su cafke Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Hakan na zuwa ne yayin da Benjamin Netanyahu ya kai ziyara Fadar White House domin ganawa da Shugaba Donald Trump.

Donald Trump da Benjamin Netanyahu
Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta bukaci Amurka ta mutunta hakkin dan Adam da kuma bin doka ta hanyar mika Netanyahu ga Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC).

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani mutumi a gidan kaso bayan kisan ƴar majalisa da mijinta

An nemi a kama Netanyahu

A cikin sakon da ta wallafa, Amnesty International da ke Najeriya ta bukaci gwamnatin Amurka ta kama Netanyahu domin gurfanar da shi.

Ta ce:

"Yayin da Netanyahu ke ziyartar White House a yau, muna tunatar da hukumomin Amurka cewa dole su mutunta hakkin dan Adam da bin doka.
"Ya kamata a cafke Firaminista Netanyahu tare da gurfanar da shi a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya."

Hakazalika, wakiliyar Amnesty International, Erika Guevara Rosas, ta sake jaddada wannan bukata, tana cewa wajibi ne Netanyahu ya fuskanci shari'a a gaban ICC kan zarge-zargen da ake masa.

An yi zanga-zanga a White House

A yayin da Netanyahu ya isa birnin Washington DC, daruruwan masu goyon bayan Falasdinawa sun taru a wajen White House domin gudanar da zanga-zanga.

Masu zanga-zangar sun daga tutocin Falasdinu tare da alluna masu dauke da sakonni irin su:

"A fallasa yadda Isra'ila ke da tasiri a Washington."

Kara karanta wannan

Trump ya lallaba ya tura bukatar tsagaita wuta Iran ta Iraq, Tehran ta yi martani

"'Yancin Falasdinawa ma yana da muhimmanci."
Benjamin Netanyahu a wajen taro
Benjamin Netanyahu da ake nema a kama a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa Netanyahu ya je Amurka ne domin ganawa da Donald Trump, wanda wannan ita ce ganawa ta takwas tsakaninsu tun bayan komawar Trump kan mulki.

Kuri'a ta nuna ra'ayin Amurkawa

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Economist/YouGov ta gudanar tsakanin ranar 25 zuwa 27 ga Yuli ta nuna cewa kashi 49% na manyan Amurkawa na goyon bayan cafke Netanyahu idan ya ziyarci kasar.

Anadolu Agency ta wallafa cewa kashi 27 sun nuna adawa da hakan, yayin da 23% suka ce ba su da wani ra'ayi a kan hakan.

Iran ta kai hari kan Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya, kuma rundunar Amurka ta yi martani.

Rundunar CENTCOM ta bayyana cewa babu wani daga cikin makaman da ya kai inda aka nufa, kuma dakarunta na ci gaba da kasancewa cikin cikakken shiri.

Daga baya rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai harin ne kan wani sansanin sojin Amurka da cibiyar rundunar CENTCOM da ke Jordan .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng