Yadda Budurwa Ta Yanke Azzakarin Saurayinta da Wuka a Kano

Yadda Budurwa Ta Yanke Azzakarin Saurayinta da Wuka a Kano

  • 'Yan sandan Kano sun kama mutum huɗu da ake zargi a wasu abubuwa biyu daban-daban da suka shafi kisa da kuma yunƙurin kashe mutum
  • An kama wasu mutum uku kan zargin dukan wani matashi har ya mutu, yayin da aka kama wata mata da ake zargin ta yanke mazakutar saurayinta da wuƙa
  • Rundunar 'yan sanda ta ce za ta gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike tare da gargadin jama'a kan ɗaukar doka a hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a wasu abubuwa biyu daban-daban da suka shafi kisa da kuma yunƙurin kashe mutum a jihar.

Mutanen da aka kama sun haɗa da wasu mutum uku da ake zargi da dukan wani matashi har ya mutu a yankin Sheka, da kuma wata mata da ake zargin ta yanke mazakutar saurayinta bayan ta gano yana shirin auren wata mace.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta saki sunayen mutane 5 da take nema ruwa a jallo

Budurwar da ta raunata saurayinta
Budurwar da ta yanke al'aurar saurayinta. Hoto: Abdu;llahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar Facebook ta ce rundunar ta ɗauki matakin gaggawa kan lamarin tare da fara gudanar da bincike.

An kashe matashi a Sheka

Rundunar ta bayyana cewa lamarin farko ya faru ne a ranar 24 ga Yulin 2026 bayan samun rahoton cewa an yaudari wani matashi mai suna Abubakar Auwal zuwa wani wuri bisa zargin yana hulɗa da matar aure.

A cewar 'yan sanda, da suka isa wurin sun tarar da matashin cikin mawuyacin hali bayan an yi masa mugun duka, sannan aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

An kama Abubakar Ali, Sulaiman Lawan da Hafsat Umar a wurin da lamarin ya faru, yayin da aka ajiye gawar mamacin a ɗakin adana gawa domin gudanar da bincike.

Budurwa ta yanke azzakarin saurayi

A wani lamarin daban, rundunar ta ce ta kama wata mata mai suna Maimunatu Idris mai shekaru 25 bayan zargin cewa ta kai wa saurayinta hari da wuƙa a wani otal da ke Badawa.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan daba sun mamaye jami'an INEC, sun sace katunan zabe

Rahoton Punch ya nuna cewa matar ta aikata hakan ne bayan ta gano saurayin nata na shirin auren wata mace, lamarin da ya sa ta yanke masa azzakari da wuƙa.

'Yan sanda sun ce an kama matar tare da ƙwato wuƙar da ake zargin ta yi amfani da ita, yayin da aka garzaya da saurayin zuwa Asibitin Abubakar Imam domin ci gaba da kula da lafiyarsa.

Abdu;llahi Haruna Kiyawa
Kakakin 'yan sandan jihar Kano. Hoto: Abdu;llahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi Allah wadai da duka abubuwan da suka faru tare da gargadin jama'a da su guji ɗaukar doka a hannu.

Ya tabbatar da cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike kuma za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Wata mata ta ƙona kishiyarta

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta kama wata mata mai suna Rabi Abubakar bisa zargin zuba wa kishiyarta mai juna biyu ruwan zafi yayin wata takaddama.

Rahotanni sun ce matar mai juna biyu ta haihu bayan harin, amma jaririn ya rasu sakamakon mummunan raunin da ya samu, yayin da rundunar 'yan sanda ta ce ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Bauchi ya ce an samu rahoton faruwar lamarin ne daga ofishin 'yan sanda na Dabe kuma ana ci gaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng