Ministan Tsaro Ya Yi wa Sojoji Albishir, Tinubu zai Sanar da Karin Albashinsu
- Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce Shugaba Bola Tinubu zai sanar da sabon karin albashin sojoji da ke kare rayukan jama'a
- Wannan karin na bayan an yi tur da gwamnatin Najeriya da ta ce ta na biyan sojoji albashi N100,000 duk da dama da su ke yi da ɓata-gari
- Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin inganta jin dadin sojoji da iyalansu saboda irin sadaukarwar da suke yi domin karfafa masu gwiwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon karin albashi ga jami'an rundunar sojin Najeriya nan ba da jimawa ba.
Christopher Musa ya bayyana hakan ne a wani taron horaswa na kwana guda da kuma tallafa wa zawarawa da matan jami'an soja da aka gudanar a Barikin Lungi da ke Abuja.

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da cewa ana ba sojoji albashi mai kyau saboda irin sadaukarwar da suke yi wajen kare Najeriya.
Minista ya yi magana kan albashin sojoji
A ruwayar jaridar The Nation, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce a makonnin da suka gabata, ya ce sojoji yanzu suna karbar N100,000, kuma ya san hakan ya jawo martani masu kyau da marasa kyau.
Ya kara da cewa:
"Lokacin da nake Babban Hafsan Tsaro, sojoji suna karbar N49,000. Kimanin shekara biyu da suka wuce na matsa lamba aka kara zuwa N100,000."
A cewarsa:
"Yanzu muna ci gaba da kokarin sake kara albashin. Mun san Shugabanmu uba ne mai sauraro wanda ya fahimci irin sadaukarwar da dakarunmu suke yi, kuma ya kuduri aniyar tabbatar da cewa suna samun albashi mai kyau. Don haka ina da yakinin cewa nan ba da jimawa ba Shugaban kasa zai sanar da wani sabon karin albashi ga dakarunmu."
An raba wa matan sojoji tallafi
Taron da Ministan ya halarta a inda ya yi wannan bayani, an shirya shi ne da fatan taken taimakon matan sojoji tare da hadin gwiwar Ma'aikatar Tsaro da SMEDAN.
Ministan ya ce shirin ya nuna kudirin gwamnatin tarayya na inganta tattalin arzikin iyalan sojoji, musamman zawarawa.
Shirin zai kuma taimaki matan jami'an da ba su kai matsayin hafsoshi ba, wadanda mazajensu ke aiki a wuraren da ake gudanar da yaki a sassan kasar.

Source: Facebook
Ya ce duk da cewa sojoji na fuskantar kalubalen tsaro masu sarkakiya kuma suna shafe lokaci mai tsawo ba tare da iyalansu ba, gwamnati ta san muhimmiyar rawar da matansu da sauran 'yan uwansu ke takawa wajen kara musu kwarin gwiwa.
Janar Christopher Musa ya bayyana cewa rundunar soja mai karfi ba ta ta'allaka kan makamai da horo kadai ba, har ma da samun iyalai masu kwanciyar hankali da ingantaccen tattalin arziki.
Yan bindiga da kayan sojoji sun kai hari
A baya, mun kawo labarin cewa yn bindiga da ake zargin sun sanya kayan sojoji sun kai hari Unguwan Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto.
Maharan da yawansu ya kai kusan 200 sun kwashe kusan sa'o'i shida suna wawushe kaya a gidaje da shaguna tare da sace dabbobin mazauna yankunan.
'Yan bindigar sun kai harin ne jim kadan bayan sojoji sun bar kauyen bayan sun mayar da martani kan wani hari da aka kai da rana domin ceto rayukan jama'a.
Asali: Legit.ng


