Mutane Na Shan Kebura, Gwamnan PDP Zai Runtumo Bashin N150bn Kan Muhimmin Abu 1

Mutane Na Shan Kebura, Gwamnan PDP Zai Runtumo Bashin N150bn Kan Muhimmin Abu 1

  • Yayin da ake fama da matsin tattalin arziki a kasar, gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin Seyi Makinde tana shirin ciyo bashin kudade masu yawan gaske
  • Gwamna Makinde ya bukaci majalisar dokokin jihar ta sahale masa karbo bashin naira biliyan 150 daga
  • Makinde ya ce za a yi amfani ne da kudaden da za a ciyo bashin ne wajen kammala aikin titin Rashidi Ladoja don rage cunkoson ababen hawa a cikin babban birnin Ibadan

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Gwamnan jihar Oyo - Seyi Makinde ya mika bukatar ciyo bashi ga majalisar dokokin jihar, wanda yawan kuɗin ya kai Naira Biliyan 150, daga wata cibiyar hada-hadar kudi ta Afrexim da Access.

Kara karanta wannan

Abin ya yi wa Ganduje yawa bayan rasa Kano, ya na fuskantar barazana a kotu kan zaben jihar APC

Gwamnan ya ce ciyo bashin zai taimaka wajen inganta harkar sufuri a jihar, tare da kammala aikin hanyar Rashidi Ladoja wadda zata taimaka sosai wajen rage cinkoson ababan hawa.

Gwamnan Oyo na shirin ciyo bashin naira biliyan 150
Mutane Na Shan Kebura, Gwamnan PDP Zai Runtumo Bashin N150bn Kan Muhimmin Abu 1 HYoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Gwamna Makinde ya aika wasika majalisar Oyo

Kakakin majalisar dokokin jihar ta Oyo, Debo Ogundoyin ne ya sanar da hakan, yayin da yake karanta wasikar da gwamnan ya aikewa da zauren ta neman amincewarsu, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar TheCable ta rahoto cewa zaman majalisar dai ya samu halartar mambobinta 20 daga cikin 32 da take da su.

Ogundoyin ya ce yana daga cikin alfanun amincewar zauren domin ciyo bashin zai taimaka wajen zamanantar da hanyoyin jihar baki daya.

Wasu abubuwa majalisar ke bukata daga bangaren zartarwa?

Daga nan sai ya mika bukata ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar, Kan cewa akwai bukatar su kara bayar da cikakken bayanin dangane da ciyo bashin, da kuma mika bayanan ga kwamitin majalisar.

Kara karanta wannan

Matakai 2 da Shugaba Tinubu ya dauka sun sa za a adana Naira Tiriliyan 8 a shekara

Ogundoyin ya ce:

"Majalisar na bukatar bangaren zartarwa su kara bayani dangane da wannan bashi, wannan kuwa ya hada da lokacin biyan bashin, da kuma nawa za a biya idan an Ttshi mayar da bashin.
"Ku bamu karin bayani kan zuwa yaushe aikin zai kammala, kuma sannan nawa ne daga cikin kudin za a kashe domin kammala aikin."

Kakakin majalisar ya Kara da cewa:

"Muna kuma neman bangaren zartarwa ya gaya mana, ta fuskar da kammala aikin zai taimakawa jihar mu, domin bunkasa tattalin arziki dama dagawar asusun tattara kudaden harajin mu."

Makinde ya magantu kan fashewar abu a Ibadan

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa abin fashewar da ya girgiza babban birnin jihar Ibadan, a daren ranar Talata, na iya zama aikin masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a jihar.

A cikin wani bidiyo, Makinde ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wasu masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, sun aje abubuwan fashewa a ɗaya daga cikin gidajen da fashewar ta auku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel