Atiku Ya Gano Abin da Ya Jawo aka Hallaka Mutum 17,000 a Mulkin Tinubu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da kin fitar da kudaden tsaro da Majalisa ta amince da su
- Atiku ya ce sama da mutum 17,000 sun rasa rayukansu tun bayan hawan gwamnatin Tinubu, yana danganta hakan da gazawar aiwatar da kasafin kudin tsaro
- Ya kuma yi alkawarin cewa idan gwamnatin ADC ta hau mulki, za ta gyara tsarin tsaro tare da tabbatar da cewa ana fitar da duk kudaden tsaro a kan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa rashin fitar da kudaden tsaro da aka ware a kasafin kudi ne ya haddasa mutuwar sama da mutum 17,000 tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya karbi mulki.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Talata 28 ga watan Yuli, 2026.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya ce kalaman Sanata Mohammed Tahir Monguno na APC sun tabbatar da abin da 'yan adawa suka dade suna zargi game da yadda ake tafiyar da kudin gwamnati.
Atiku ya dura a kan agwamnati
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Atiku ya ce bayanan da Monguno ya yi sun nuna illar rashin gudanar da harkokin kudi yadda ya kamata, lamarin da ya ce yana daga cikin dalilan da suka sa matsalar tsaro ke ci gaba da salwantar da rayukan 'yan Najeriya.
Ya ce rahotanni daga masu sa ido kan rikice-rikice sun nuna cewa fiye da mutum 17,000 ne aka kashe tun bayan fara mulkin Tinubu, yayin da dubban wasu suka fada hannun 'yan ta'adda, 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
A cewarsa:
"Waɗannan ba alkaluma ba ne kawai. Uwaye ne, iyaye ne, yara ne, manoma ne, dalibai ne da masu ciyar da iyalansu da aka kashe. A bayan kowane adadi akwai iyalin da za su rayu cikin bakin ciki har abada."
Atiku ya ce tsawon lokaci APC na kallon korafe-korafen 'yan adawa kan aiwatar da kasafin kudi da kudaden tsaro a matsayin siyasa, amma yanzu daya daga cikin manyan sanatocin jam'iyyar ne ya fara tambayoyin da 'yan Najeriya suka dade suna yi.
Ba da kudin tsaro dole ne - Atiku
Atiku ya ce idan ba a bai wa hukumomin tsaro kudaden da doka ta tanada domin sayen kayan aiki, inganta tattara bayanan sirri, dabarun aiki da gudanar da ayyuka ba, gwamnati ba za ta iya kubuta daga alhakin abin da ya biyo baya ba

Source: Twitter
Ya kuma ce abin mamaki ne yadda Tinubu, wanda ya dade yana sukar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan matsalar tsaro, yanzu yake jagorantar gwamnatin da ke jiran a kashe mutane kafin ta rika mika sakon ta'aziyya.
Atiku ya yi alkawarin cewa idan ADC ta kafa gwamnati karkashin jagorancinsa, za ta sake fasalin tsarin tsaron Najeriya, data tabbatar da ana sakin duk kudaden tsaro cikin gaggawa.
Ya kara da cewa zai kuma inganta aikin tattara bayanan sirri, a samar da fasahar sa ido ta zamani, a karfafa tsaron kan iyakoki, da inganta hadin gwiwar hukumomin tsaro.
Atiku ya yi wa Babachir martani
A baya, mun kawo labarin cewa dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da kalaman tsohon sakataren gwamnatin tarayya a zamanin Muhammadu Buhari, Babachir lawal.
Alhaji Atiku Abubakar ya ce Babachir na neman haddasa rabuwar kai tsakanin 'yan Najeriya, yana mai cewa bai kamata ya nuna kabilanci a harkar tafiyar da siyasar kasar nan mai dimbin mutane da yaruka da dama ba.
A cewarsa, idan aka bi irin wannan tunanin, za a iya dora wa kowace kabila laifukan da wasu tsiraru daga cikinta suka aikata, lamarin da zai iya haifar da rabuwar kai a kasa, wanda zai zama matsala a Najeriya.
Asali: Legit.ng


