Iran Ta kai Harin ba Zata kan Amurka yayin da Trump Ya Gana da Netanyahu
- Iran ta kai wani harin ba-zata da makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya, amma Amurka ta ce an dakile dukkan makaman
- Rundunar CENTCOM ta ce babu wani makami da ya samu nasarar kai wa inda aka nufa, yayin da sojojin Amurka suka ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana
- Harin ya zo ne bayan Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta dakatar da hare-haren Iran, duk da cewa Tehran ta musanta cewa tana tattaunawa da Washington
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa Iran ta kai wani harin ba-zata da makamai masu linzami kan dakarunta da ke Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa duk da harin, rundunar tsaron Amurka ta samu nasarar cafke dukkan makaman da Iran ta harba ba tare da sun yi wata barna ba.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa harin ya kara dagula halin da ake ciki a yankin, a daidai lokacin da ake kokarin farfado da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran.
Yadda Iran ta kai harin
Rundunar CENTCOM ta bayyana a wata sanarwa cewa dakarun rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) sun harba makamai masu linzami da dama da misalin karfe 5:45 na yamma.
Al Jazeera ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
"IRGC ta harba makamai masu linzami da dama daga Iran a wani yunkurin kai harin ba-zata kan dakarun Amurka da ke Gabas ta Tsakiya."
"Dukkan makaman an samu nasarar cafke su, kuma dakarun Amurka na ci gaba da kasancewa cikin cikakken shirin ko-ta-kwana."
CNN ta ruwaito cewa jami'an Amurka sun ce alkaluman farko sun nuna cewa Iran ta harba makamai masu linzami guda hudu ko kasa da haka.
Harin ya zo bayan kalaman Trump
Harin ya faru ne kusan kwana guda bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka ta dakatar da kai hare-hare kan Iran, yana mai cewa Tehran na son bude kofar tattaunawa.
Sai dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya musanta hakan, yana cewa:
"A halin yanzu ba mu da wata tattaunawa da Amurka."

Source: Facebook
A lokaci guda kuma, shugaban Amurka ya gudanar da ganawa ta sirri da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, inda aka tattauna batun Iran da sauran matsalolin tsaro.
Haka kuma Iran ta sanar da cewa tana kara habaka kera makamai, yayin da ta gargadi cewa za ta hana jiragen ruwa na kasashen da ke amfani da kadarorinta da aka daskarar wucewa ta mashigar Hormuz.
Masu taimakon Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta zargi wasu kasashen yankin da taimaka wa Amurka wajen kai hare-haren soji kan kasarta ta hanyar ba ta damar amfani da yankunansu.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce Tehran na ci gaba da son kyakkyawar alaka da makwabtan kasashe, amma ba za ta manta da rawar da wasu suka taka ba.
Ya bayyana cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin Iran da kasashen yankin Gulf, wanda zai iya zama tubalin kara karfafa amincewa da hadin kai.
Asali: Legit.ng
