Elon Musk Ya Ce a 2036 za a Dawo Rayuwa ba Tare da Bukatar Kudi Sosai ba

Elon Musk Ya Ce a 2036 za a Dawo Rayuwa ba Tare da Bukatar Kudi Sosai ba

  • Attajirin duniya Elon Musk ya yi hasashen cewa kuɗi ba za su ƙara zama masu muhimmanci ba nan da shekaru 10 saboda ci gaban AI da mutum-mutumi
  • Musk ya ce injuna za su riƙa samar da kayayyaki da ayyuka fiye da yadda mutane za su iya amfani da su, lamarin da zai sauya tsarin tattalin arziki
  • Elon Musk ya kuma yi magana kan siyasa, zargin nuna wariya da kuma makomar fasahar AI, yana mai cewa bai damu da masu sukarsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya bayyana cewa nan da shekaru 10 masu zuwa kuɗi ba za su ƙara zama masu muhimmanci ba.

Ya fadi haka ne saboda irin gagarumin ci gaban da ake samu a fannin basirar AI da kuma mutum-mutumin za a rika samu sosai.

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganganu da aka 'gano' makaman Amurka na neman karewa

Attajirin duniya, Elon Musk
Wanda ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Elon Musk ya bayyana hakan ne yayin wata hira da mujallar The Economist, inda ya yi bayanin yadda fasaha za ta sauya tattalin arzikin duniya da aiki gaba ɗaya.

'Kudi za su rage tasiri,' Musk

A cewar shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX, idan mutum-mutumi da AI suka fara samar da kayayyaki da ayyuka fiye da yadda mutane za su iya amfani da su, to bukatar kuɗi za ta ragu ƙwarai.

Ya ce:

"Me ake buƙatar kuɗi domin shi? Domin sayen kayayyaki da ayyuka. Idan mutum-mutumi da AI suna samar da fiye da abin da mutane za su iya amfani da shi, to me za a yi da kuɗi?"

Musk ya ƙara da cewa maimakon mutane su shiga cikin matsin tattalin arziki saboda AI, fasahar za ta iya haifar da abin da ya kira "babban wadatar rayuwa ga kowa," inda injuna za su riƙa yin mafi yawan ayyukan samar da arziki.

Kara karanta wannan

Fitaccen mai barkwanci a Najeriya, AY ya daina zuwa coci, ya fadi abin da ya faru

Magana kan nuna wariya

Musk ya kuma yi magana kan rawar da ya taka a gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump bayan an naɗa shi babban mai ba shugaban ƙasa shawara kuma jagoran hukumar DOGE, wadda aka kafa domin rage almubazzaranci da kuɗi gwamnati.

Ya ce ya fuskanci suka da dama saboda matsayarsa ta siyasa, amma ya musanta zargin cewa shi mai nuna wariyar launin fata ne.

Elon Musk a wajen wani taro
Attajiri Elon Musk yana magana a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewarsa, yana da yara da abokiyar rayuwa 'yar asalin Indiya, kuma kamfanoninsa na ɗauke da manyan jami'ai daga kabilu daban-daban.

Kudin Musk ya karu sosai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Elon Musk na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun 'yan kasuwa da suka fi jan hankali a duniya saboda tasirinsa a fannin fasaha da kasuwanci.

Duk da kasancewarsa mutum na farko da ya kai matsayin dala tiriliyan 1, Musk na ci gaba da samun goyon baya daga dimbin mutane, yayin da wasu ke sukar yadda yake tsoma baki a harkokin siyasa.

Masana na ganin salon maganganunsa da yadda yake bayyana ra'ayinsa ba tare da ɓoye komai ba na daga cikin abubuwan da suka sa yake ci gaba da zama abin ce-ce-ku-ce a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng