Binciken Zargin Kisan Kai 5 Da Suka Girgiza Jihar Kano

Binciken Zargin Kisan Kai 5 Da Suka Girgiza Jihar Kano

Jihar Kano - A cikin shekaru biyar da suka wuce, an samu matsalolin kisan kai da suka tayar da hankali a Kano.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wasu daga ciki sun dauki hankulan mutanen kasar baki daya ba iya jihar kadai ba da abin ya faru.

Jerin shari'o'in kisan kai a Kano da ke gaban kotu
An sha samun kisan kai a Kano wadanda suka tayar da hankali matuka. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Jerin shari'o'in da ke gaban kotu

Wanda ya fi daukar hankula a baya-bayan nan shi ne wanda wata matar aure mai suna Hafsat 'Chuchu' ta hallaka matashi mai suna Nafi'u Hafiz.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku manyan laifukan kisan kai a jihar guda 5 mafi daukar hankali.

Kara karanta wannan

Matashi ya gurfana a kotu kan zargin taba muhibbar malamin addini a Kano

1. Nafi'u Hafiz/Hafsat 'Chuchu'

Yaduwar labarin kisan da matar aure Hafsat 'Chuchu' ta yi wa wani matashi da ake zargin yaron gidan ne ya tayar da hankulan mutane da dama.

Marigayin mai suna Nafi'u Hafiz ya gamu da ajalinsa a watan Disambar 2023 bayan matar ta caccaka masa wuka a wuya.

Rundunar 'yan sanda daga bisani ta yi nasarar cafke matar tare da mijinta da ake zargi da hadin baki a kisan, cewar Vanguard.

Yanzu haka ana kan shari'ar kisan kai din a kotun majistare a Kano wacce ta umarci ci gaba da tsare Hafsat a gidan kaso.

2. Imam Sani Muhammad/Matashi

Kisan Imam Sani Shu'aibu ya fi muni inda wani matashi ya daba masa wuka a Unguwar Jakara da ke Kano.

'Yan sanda sun yi nasarar cafke matashin wanda ya yi ajalin limamin bayan ya gargade shi kan shan tabar wiwi a gefen masallacin.

Kara karanta wannan

Kano: Mota ta murkushe mai kwacen waya jim kadan bayan fauce wayar wata, ya shiga kakani-kayi

Yanzu haka ana kan shari'ar inda aka dage sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Janairu.

3. Alkasim Ya'u/Ya'u Mohammed

Hukumar NSCDC ta cafke dan shekaru 25 mai suna Alkasim Ya'u kan zargin hallaka mahaifinsa a Tudun Yola da ke karamar hukumar Gwale a Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mahaifin yaron ya kawo shi asibitin kwakwalwa a Dawanau don samar masa lafiya.

An tabbatar da cewa yaron na fama da cutar kwakwalwa ne saboda ta'ammali da miyagun kwayoyi.

4. Ummulkulsum Buhari/Geng

A watan Disambar 2022, wani dan China mai suna Geng Quangrong ya hallaka budurwarsa mai suna Ummulkulsum Buhari a Kano.

Masoyan sun shafe shekaru biyu suna soyayya kafin samun matsala wanda hakan ya fusata Geng har ya dauki matakin a kanta.

5. Amina Bala/Ukasha/Chidera

'Yan sanda sun cafke Ukasha Mohammed da Chidera Ugwu kan zargin zubar da cikin wata budurwa.

A dalilin haka, budurwar mai suna Amina Bala ta rasa ranta a ranar 20 ga watan Disamba, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yusuf vs Gawuna: Sabon hasashe ya nuna wanda zai yi nasara a Kotun Koli a shari'ar Kano

Ana zargin Ukasha da dirka mata ciki yayin da Chidera shi ne likitan bogi da ya yi kokarin zubar da cikin.

Mai kwacen waya ya mutu a Kano

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a Kano ta tabbatar da mutuwar matashin da ya kwace wayar wata mata.

Matashin ya gamu da tsautsayi ne bayan kwace wayar inda mota ta buge shi inda ya rasu daga baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel