Yan Bindigan da Suka Sace Mutane a Abuja Sun Canza Wuri, Sun Aiko Sako Mai Daga Hankali

Yan Bindigan da Suka Sace Mutane a Abuja Sun Canza Wuri, Sun Aiko Sako Mai Daga Hankali

  • A farkon makon jiya ne masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da mutum 23 a kauyen Kawu da ke Bwari, babban birnin tarayya Abuja
  • Zuwa yanzu maharan sun tisa keyar mutanen daga Abuja zuwa wani daji a garin Akilbu da ke jihar Kaduna
  • Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi yan uwan wadanda abun ya ritsa da su, inda suka bukaci a kawo masu kayan abinci da babura guda biyar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Masu garkuwa da mutanen da suka sace mutum 23 a kauyen Kawu, yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja, sun tisa keyar wadanda suka sace zuwa wani jeji a garin Akilbu.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

Bayan komawa da mutanen garin Akilbu da ke hanyar titin Kaduna zuwa Abuja, maharan sun kuma bukaci yan uwansu da su kawo masu babura biyar da kayan abinci.

Yan bindiga sun bukaci a kawo masu babura da kayan abinci
Yin bindiga sun bukaci yan uwan wadanda suka sace su kawo babura 5. Shinkafa, wake da sauransu Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A ranar Talata da ta gabata ne masu garkuwa da mutanen suka farmaki yankin Kawu sannan suka yi awon gaba da mutum 23, ciki harda mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, yan bindigan sun sako mutum hudu daga bisani tare da neman a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansarsu.

Me da me yan bindigan suka nema?

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho a ranar Talata, Malam Mu’azu Alhassan, dan uwan daya daga cikin mutanen da aka sace, ya ce maharan sun kira a ranar Litinin.

Haka kuma, Malam Alhassan ya ce sun bukaci iyalin su siya masu kayan abinci.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Alhassan ya ce:

"Jiya jiyan nan, kasancewarsa Litinin, shugaban yan bindigar ya kira cewa mutanen da ke tsare a hannunsu suna dajin Akilbu kuma cewa suna bukatar shinkafa, wake, katan din taliya uku da jarkan manja."

Ya kara da cewar yan bindigar sun kuma bukaci yan uwan mutanen da abun ya ritsa da su, su kawo masu babura guda biyar, rahoton Trust Radio.

Yan bindiga sun sace mutum 85

A wani labarin, mun ji cewa an yi garkuwa da a kalla mutane 85 yayin da yan bindiga suka kai hare-hare garuruwa da dama a jihar Kaduna.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, hare-haren sun gudana ne tsakanin Alhamis, 4 ga watan Janairu da Lahadi, 7 ga watan Janairu.

Jaridar ta bayyana cewa wakilanta da suka ziyarci titin Kaduna zuwa buja a Dogon Fili kusa da Katari a jihar Kaduna, a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, sun tattaro cewa kimanin matafiya sama da 30 aka sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel