Tsohon Sanatan APC Ya Bayyana Dalili 1 da Zai Hana Yan Najeriya Karanta Littafin Buhari

Tsohon Sanatan APC Ya Bayyana Dalili 1 da Zai Hana Yan Najeriya Karanta Littafin Buhari

  • A ranar Talata, 16 ga watan Janairu ne, Femi Adesina, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani littafi
  • Adesina ya kaddamar da littafin ne a babban birnin tarayya Abuja domin karrama tsohon ubangidan nasa
  • Sai dai, Shehu Sani ya ce yan Najeriya basa bukatar karanta wannan littafin domin dai su ganau ne, sun dandana mulkin da kansu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya ce yan Najeriya basa bukatar karanta littafin nan da tsohon mai magana da yawun shugaban Muhammad Buhari wato Femi Adesina ya wallafa.

Shehu Sani wanda dan gwagwarmaya ne, ya ce tuntuni mulkin shekaru takwas din Buhari ya zama jiki magayi, domin kuwa ko dan yaro ya san cewa an yi mulki a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Daga yin kwana 7 har Tinubu ya shure umarnin da ya bada domin rage facakar kudi

Shehu Sani ya ce yan Najeriya sun ji a jikinsu a mulkin Buhari
Tsohon Sanatan APC Ya Bayyana Dalili 1 da Zai Hana Yan Najeriya Karanta Littafin Buhari Hoto: @ShehuSani/@BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ya ce tuni yan Najeriya suka kasance a yanayin da sunan littafin ya tafi akai, wato cukumurdar shugabancin Buhari ga yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata, 16 ga watan Janairu ne, Femi Adesina ya kaddamar da littafin da ya rubuta wanda ya yiwa take da "Aiki na da Buhari a matsayin Mai magana magana da yawunsa na musammaan daga 2015-2023".

Taron kaddamar da littafin ya samu halartar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, da kuma wanda ya gaje shi, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Da yake wallafa ra'ayinsa dangane da littafin, a shafinsa na X Sani ya ce Yan Najeriya su ganau ne ba jiyau ba a kan mulkin Buhari.

Sani ya rubuta a shafin nasa:

"'Yan Najeriya ba sa bukatar karanta littafin Buhari saboda yanzu kowa yana rayuwa a kan rubutun littafin tun daga farkonsa zuwa ga bayyanarsa mai cike da rudani."

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana matsayarsa kan mulkin Bola Tinubu da APC a taron Abuja

Buhari ya nemi afuwar yan Najeriya

A gefe guda, Legit Hausa ta kawo a baya cewa watanni bakwai da yin ban kwana da karagar mulki, Muhammadu Buhari, ya fito ya yi magana a game da gwamnatinsa.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yarda ya kawo wasu tsare-tsare da suka wahalar da al’umma, Premium Times ta kawo labarin.

Tsohon shugaban na Najeriya ya ce halin da aka shiga ne ya jawo dole ya ba jama’a hakuri daf da barin kujerar mulki a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel