Kabiru Gaya: 'Abin da Mu ka Tattauna da Shugaba Tinubu a Abuja'
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kabiru Gaya ya fito ya bayyana dalilin da ya sa aka hango shi tare da Sanata Barau Jibrin da Rufa'i Hanga a wurin Tinubu
- Ya bayyana cewa shugaban APC, Nentawe Yilwatda da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje sun kai masa ziyara a gidansa kafin ya zauna da shugaba Tinubu
- Tsohon gwamnan da aka kafa jam'iyyar APC da su ya bayyana abubuwan da ya shaida wa Bola Tinubu game da watsi da aka yi da su bayan an ci zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kabiru Gaya, tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar NDC, ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya kai masa ziyara a gidansa domin neman ya sauya sheka zuwa APC.
A cewarsa, Yilwatda ya shaida masa cewa daga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu har zuwa sauran manyan shugabannin APC, babu wanda bai san da shi ba.

Source: Facebook
A hira da ya yi da BBC Hausa, Sanata Kabiru Gaya ya ƙara da cewa, bayan wannan ziyara ce tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya je gidansa domin ci gaba da tattaunawa kan batun komawarsa jam'iyyar APC.
Kabiru Gaya ya tuno rawarsa a APC
A hirar, Sanata Kabiru Gaya ya tuna yadda aka kafa jam'iyyar APC, yana mai cewa ya na cikin waɗanda suka assasa ta tare da Shugaba Bola Tinubu.
Kabiru Gaya ya ce:
"To na farko dai mun je a kan maganar ita jam'iyyar APC."
"Da ni aka kafa jam'iyyar APC. Da ni da Shugaba Tinubu duk muna mambobi, shi ne shugaban kwamitinmu na zaɓar alamar jam'iyya."

Source: Facebook
Ya ce sun yi doguwar tattaunawa kafin daga bisani aka amince da alamar tsintsiya ta zama shaidar jam'iyyar da ta karbe mulki a kasar nan.
"Mun yi musu kala-kala har aka zo aka samu tsintsiya. Mu ka kafa jam'iyya, aka yi zaɓe, mu ka ci zaɓe."
An tattauna tsakanin Kabiru Gaya da Hanga
Ya ce bayan Ganduje ya bar gidansa, daga baya aka kira shi daga ofishin Shugaban Ƙasa, inda aka gayyace shi ya je ganawa da Tinubu tare da Sanata Barau Jibrin da Sanata Rufai Hanga
A cewarsa, a yayin ganawar ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa su ne aka yi watsi da su, amma shugaban ƙasar ya musanta hakan.
Kabiru Gaya ya bayyana cewa ba a tattauna da su kan wasu sharudda ko alƙawuran da za a cika idan suka koma APC ba. Sai dai ya ce Tinubu ya shaida masu cewa ya kamata su ci gaba da kasancewa cikin gwamnatin da suka taimaka wajen kafawa.
Da aka tambaye shi abin da ya sa ya koma APC, Kabiru Gaya ya ce matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga kishin ƙasa da kuma son yi wa al'umma hidima.
A kalamansa:
"A halin yanzu wannan buƙata ta neman takarar Sanata ai ta ƙare, domin an gama zaɓen fitar da gwani, an fitar da 'yan takara. Babu wani abu da ya rage."
Ya ƙara da cewa duk wata dama da jam'iyyar APC za ta ba shi domin ya taimaka wa jam'iyyar, a shirye yake ya karɓa ba tare da matsala ba.
Tinubu ya ga Kabiru Gaya da Hanga
A baya, kun samu labarin cewa Sanata Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci Hanga da tsohon Sanata Kabiru Gaya zuwa ganawar da suka yi da Tinubu yayin da ake rade-radin za su koma APC.
Majiyoyi masu tushe sun shaida cewa waɗannan ganawa na daga cikin shawarwarin da ake yi dangane da yiwuwar komawar Hanga da Sanata Kabiru Gaya daga jam'iyyar NDC zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng


