Jama'a Sun Kadu Bayan Kama Mahaifi da Niyyar Cefanar da Ɗan Cikinsa Kan N20m, Ya Fadi Dalilin Haka

Jama'a Sun Kadu Bayan Kama Mahaifi da Niyyar Cefanar da Ɗan Cikinsa Kan N20m, Ya Fadi Dalilin Haka

  • Abun mamaki baya karewa a duniya yayin da aka kama mahaifi da kokarin siyar da ɗan cikinsa mai shekaru shida
  • Wanda ake zargin mai suna Chinana Talida ya yi kokarin siyar da ɗan cikinsa kan kudi naira miliyan 20 a birnin Abuja
  • Kwamandan hukumar a yankin Abuja, Olusola Odumosu shi ya bayyana haka a jiya Talata 17 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta NSCDC ta cafke wani mutum da zargin yin garkuwa da ɗan cikinsa a Abuja.

Hukumar na zargin Chinana Talida da kokarin siyar da ɗan nashi naira miiiyan 20 a birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Tinubu zai yi garambawul a kujerun Ministoci? Gaskiya ta fito

NSCDC ta cafke wani da zargin kokarin siyar da ɗan cikinsa a Abuja
An Kama Mahaifi da Niyyar Siyar da Ɗan Cikinsa Kan N20m. Hoto: NSCDC.
Asali: Twitter

Yaushe NSCDC ta kama wanda ake zargin?

Kwamandan hukumar a yankin Abuja, Olusola Odumosu shi ya bayyana haka a jiya Talata 17 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Odumosu ya ce sun yi nasarar cafke mutumin ne a wurin da ya ke kokarin siyar da yaron bayan ya shigo da shi daga jihar Benue zuwa birnin Abuja.

Daily Trust ta tattaro cewa yayin bincike wanda ake zargin ta ce yaron mai suna Ushafa Tali ɗan cikinsa ne mai shekaru 6 a duniya.

Ya ce ya na da 'ya'ya 6 inda ya yi tunanin siyar da daya don neman kudin da zai kula da iyalansa yadda ya kamata.

Wane martani wanda ake zargin ya yi?

Ya ce:

"Saboda halin da muke ciki ne kuma babu kudi, ina bukatar kudi don kula da tarbiyan sauran yaran."

Kara karanta wannan

Kano: Mota ta murkushe mai kwacen waya jim kadan bayan fauce wayar wata, ya shiga kakani-kayi

Hukumar ta ce ta yi nasarar cafke mutumin ne bayan samun bayanan sirri a yankin, cewar Daily Post.

Ta ce a kokarin mahaifin na neman wanda zai fi biyan kudade masu yawa kan yaron ne ya sa aka yi nasarar cafke shi.

Mai kwacen waya ya mutu a Kano

A wani labarin, wani matashi mai kwacen waya ya gamu da tsautsayi bayan mota ta murkushe shi a birnin Kano.

Matashin ya kwace wayar wata mata inda ya yi kokarin tsallaka titi a lokacin ne mota ta buge shi.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da cewa matashin ya rasu bayan samun raunuka a jikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel