Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Soja a Abuja, an Raunata Matarsa da Wasu
- Wasu 'yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude na rundunar sojin Najeriya a gidansa da ke Kurudu, Abuja, bayan dawowarsa daga aiki da yammacin Litinin
- Matar mamacin, direbansa da jami'in tsaronsa sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawa
- Hukumomin tsaro da rundunar soji sun fara bincike domin gano maharan, yayin da har yanzu ba a bayyana musabbabin harin a hukumance ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Wasu 'yan bindiga sun kashe wani Kanal mai aiki a rundunar sojin Najeriya, Abdussalam Ude, a wani hari da suka kai gidansa da ke yankin Kurudu a Abuja.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin Litinin, jim kaɗan bayan Kanal Ude ya dawo gida daga wurin aikinsa.

Source: Facebook
Yadda ƴan bindiga suka yi yunkurin sace ahi
Rahotanni sun ce maharan sun yi yunƙurin sace Kanal Ude ko kuma wasu daga cikin iyalansa kafin al'amura suka rikide zuwa harbe-harbe, cewar Vanguard.
A yayin harin, Kanal Ude ya mutu sakamakon harbin bindiga, yayin da matarsa, direbansa da jami'in tsaronsa suka samu raunuka.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, yayin da ake ci gaba da bibiyar lafiyarsu.
Har yanzu ba a tabbatar da ainihin dalilin harin ba, kuma hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan abin da ya jawo lamarin ba.
Majiyoyin da ke da masaniya sun ce jami'an tsaro da hukumomin rundunar soji sun fara bincike domin gano waɗanda suka kai harin.

Source: Original
Gudunmawar da marigayin ya bayar ga rundunar
An ce Kanal Ude ɗan asalin Enugu ne, kuma ya yi aiki a sashen leƙen asirin rundunar sojin Najeriya tare da riƙe muƙamai masu muhimmanci.
Rahotanni sun nuna cewa ya halarci ayyukan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabashin Najeriya, sannan ya yi aiki a ƙasashen Chadi da Faransa.
Abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin ƙwararren soja mai jajircewa da sadaukar da kai wajen gudanar da aikinsa cikin gaskiya da ƙwarewa.
Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba, yayin da ake sa ran ƙarin bayani bayan bincike.
Karin bayani na tafe....
Yan bindiga sun kashe tsohon soja a Nasarawa
A baya, mun ba ku labarin cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari wata unguwa da ke kan iyakar Abuja da Nasarawa, inda suka sace wata mata da tsakar dare.
Wani tsohon sojan Najeriya ya fito domin taimakawa lokacin harin, amma maharan sun harbe shi har ya mutu nan take lamarin da ya tayar wa jama'ar yankin hankali.
Rundunar ƴan sanda ta fara bincike, yayin da jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi domin ceto matar da aka sace tare da kamo waɗanda suka kai harin.
Asali: Legit.ng

